A yayin da ake shirye-shiryen fara zaben shekarar 2019, Gidauniyar tallafawa gajiyayyu ta daya daga cikin 'yan takarar shugabancin kasarnan karkashin jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ta baiwa tauraruwar fina-finan Hausa, Maryam Booth wani babban mukami.
Mukamin da gidauniyar ta baiwa Maryam shine na mataimakiyar shugaban ta na kasa shiyyar Arewacin Najeriya, kamar yanda sanarwar da shugaban gidauniyar ta kasa, Aliyu Bin Abbas ya fitar ta bayyana.
Muna tayata murna da fatan Allah ya taya riko.
Post a Comment