A ranar Alhamis, 20 ga watan Satumba gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ta ware wasu makudan kudade na mussaman domin tallafawa manoman shinkafa don ganin an karya farashin shinkafa yar gida.

Ministan gona da raya karkara, Cif Audu Ogbeh yace bankin noma da ma’aikatar said ne zasu kula da kudin inda ya kara da cewa gwamnati tayi wannan karamcin ne domin tabbatar da cewar shinkafa yar gida tayi araha sannan kuma tafi shinkafa yar waje farin jini a kasuwa.

Ogbeh Yayi Wannan Magana ne a lokacin wani taro na kungiyar manoman shinkafar Najeriya Rice Farmers Association of Nigeria (RIFAN) da masu sarrafa shinkafa a ofishinsa dake Abuja

@Arewarmu Ayau

Post a Comment

 
Top