Hafsat Idiris wadda wasu ke kira da Barauniya ko kuma 'yar fim na daya daga cikin taurarin fina-finan Hausa dake jan zarensu a wannan zamani, wani kishin-kishin din labari da abokin aikinta ya labarta na nuna alamar cewa jarumar ta kusa yin aure.

Nuhu Abdullahi wanda shima taurarone a masana'antar fim din Hausa ya saka hotunan Hafsat tare da me shirya fim din Hausa, Shazali Kamfa a shafinshi na sada zumunta inda ya kira su Ango da Amarya da kuma masoyan Kannywood har ma yayi addu'ar cewa Allah ya kaimu ranar.
Koma dai menene gaskiyar lamari, lokaci be bar komai ba.

Post a Comment

 
Top