Hakika ba za ka taba samun jin dadin zamantakewar aure a cikin gidanka ba har sai ka kiyaye wadansu dabi’u da za ka mu’amalanci matarka da su, don haka sai mu kiyaye su.
Hakika su mata suna son lallashi da ja a jiki, kuma suna son a dinga cewa ana sonsu ana kaunarsu. Don haka kada ka dinga yi musu rowar fadar haka, idan kuwa ka yi rowar to ka sanya hijabi tsakanin ka da ita na samun karancin soyayya da kauna. Ka sani cewa su mata ba sa son mutum mai tsananin takurawa, idan ka fahimce su, suna yi wa mutum rarrauna hidima. Don haka kowacce sifa ka a jiye ta a gurin da ta dace domin hakan shi zai fi jawo kauna da nutsuwa a tsakaninku. Hakika su ma mata suna son irin abin da namiji yake so daga gurin mace, kamar daddadan kanshi, magana mai dadi, kyakkyawar shiga, tashin kanshi da dai sauransu. To don haka ka sifantu da dukkan wadannan halaye a dukkan yana yinka.
Ka sani cewa gida wata masarauta ce ta mace wadda take jin cikyakkyen iko a cikin ta kuma take jin cewa ita ce shugaba a cikinsa. To ina jan kunnenka duk wani majidanci da kada ka kuskura ka rusa wannan masarauta, kana mai nuna mata cewa ita ba kowa bace ko kuma gidanka ne sai yadda ka so sai abin da ka so, idan ka yi haka to ka tumbuketa daga kan sarautarta, kuma mai mulki bashi da wani abokin gaba a duniya fiye da wanda ya sauke shi daga kan mulkinsa. Dukkan mace tana son ta yi wa mijinta hidima amma kuma ba ta son ta rabu da ‘yan’uwanta, to kada ka yi kokarin raba ta da danginta, ta hanyar ba ta zabin ko kai ko danginta, domin idan ta zabe ka a kan danginta to babu shakka za ka dawwama cikin bakin ciki da bacin rai da za ka dinga samu daga gare su. Hakika ita mace an halicce ta ne daga kashin hakarkarin namiji karkatacce, wannan kuma ba aibu ba ne a gare ta, shi ne ma kuma sirrin kyawunta da kuma jan hankalin da take yi wa maza, don haka kada ka hayayyako mata a lokacin da ta yi wani kuskure kana kokarin gyara ta da karfin tsiya sai ka karyata, karya ta kuwa shi ne sakinta. To kada kuma ka kyale ta ta yi abin da ta ga dama ko kuma ta ci gaba da yin kuskuren da sunan a karkace take, domin sai ta bijire maka daga karshe ta ki yi maka biyayya, kai dai ka kasance da ita baina-baina. To kuma ka sani cewa su mata sun dabi’antu a kan saba wa miji da kuma yi masa butulci.
Idan da za ka kyautatawa mace tsawon shekara ko zamani, sai wata rana ka munana mata, za ta ce me ka taba yi min?. To kada a wannan hali na ta ya sa ka kyamace ta gaba daya, domin idan ka kyamaci wannan dabi’ar daga gare ta to za ka yarda kuma da wasu halayenta masu kyau. Ita mace ba kamar namiji ba ce, tana rayuwa ne cikin rauni na jiki dana ruhi, saboda haka ne ma Allah ya dauke mata wasu daga cikin farillan da ya wajabta mata a wani lokuta saboda wannan rauni na ta. Dubi yadda Allah ya dauke mata sallah a yana yi na haila, ya jinkirta mata rama azumi har sai ta gama haila, to ka saukaka mata umarninka da hane- hanenka a wannan yana yi kamar yadda ubangijinta ya saukaka mata farillansa. Ka sani cewa ita mace baiwa ce a hannunka, don haka ka ji kanta ka tausaya mata ka kuma dauke kai dangane da rauninta sai ta zamar maka kyakkyawar abokiyar zama kuma mace ta gari. Allah ya bamu ikon zama da iyalanmu lafiya.
Sources :leadershipayau.com

Post a Comment