Gida ko muhalli waje ne mai muhimmanci musamman a wajen mai iyali, domin waje ne na hutawa daga gajiyar da mai rai ya yi wajen aikace-aikace da matsalolin rayuwa. Don haka samuwar yanayi mai kyau da ke cike da so da kauna da girmama juna ya kan mantar da mutum wahalhalun rayuwa da kuma rage masa damuwa da rashin tabbas da yake damun sa.

Wannan ne ya sa ake son aurar mace mai tausayi da hangen nesa da kuma macen da ta san ya kamata a harkokin rayuwa. Idan aka samu haka, to fa ana saran samun nasara a zamantakewar aure. Mu duba wadannan fannonin a cikin gida:

Ado Da Kwalliya: Ya halatta mace ta yi wa mijinta ado da dukkan kayayyakin ado domin jin dadin maigida. Kayayyakin da suka hada da karin gashi da sanya sarka da zobe da awarwaro da sanya janbaki da janfarce, kai har da zane a fuska, mutukar zai kara miki kyau, ko lalle da ake yi a hannu ko kafa, dukkansu abin da za su kara wa mace kyau ne, abin da kawai ba a so shi ne, ta yi su ga wanin mijinta, to wannan bai halarta ba.

Soyyaya: A cikin al’ummarmu ta Hausawa akwai masu tunanin cewa idan an yi aure, to soyyaya ta kare, wai sai a shiga sabawa juna, wanda wannan ba haka ba ne. Yana da kyau ki rika cin ado, ki shafa turare domin ki jira dawowar mijinki don ki yi masa tarba ta musamman.

Girki: Kamar yadda girki kan jawo rigima ko rikici idan bai yi dadi ba, to fa haka nan ya kankara wa aure karfi da karko idan ya yi dadi. Ana so ki iya girki kala-kala, ta yadda za ki rika canja salo lokaci bayan lokaci, misali, yau idan kin yi tuwon shinkafa, gobe kuma sai ki yi masa sinasir. Akwai littattafai da dama da suke koyar da girki, don haka ki saya domin zai taimaka miki.

Hira Da Maigida: Abu ne da yake kara dankon kauna a tsakanin ma’aurata. Ya kamata ki rika yi wa mijinki dadadan kalamai ta yadda zai ji ba ya son zama a ko’ina sai gida. Matukar kika rika barin maigidanki yana yawan fita zaman majalisa to laifinki ne.
Tsari Da Tsabta: Yana da kyau bayan kin wanke ko kin goge kayayyakin daki to sai ki tsarasu ta yadda kowanne abu za ki ajiye shi a muhallinsa.

Rikon Amana Da Rikon Sirri: Mace tagari ita ce wacce take rike amanar mijinta, misali, kada ki dauki wani abu nasa ba tare da ya sani ba, kada ki rika boye ragowar kayan abinci ba tare da sanin sa ba.

– Ya ‘yar’uwa kada mijinki ya fada miki wani sirri, ke kuma ki rika gaya wa kawayenki ko wani mutum daban, lallai fallasa sirrin gida bakaramin hadari ba ne ga rayuwar iyali.

– Ya ‘yar’uwa, ki yi kokari wajen girmama na gaba da ke, kamar mahaifiyar mijinki da mahaifin mijinki, matukar kina girmama su, mijinki zai kara kaunarki. Haka ya kamata ki rika ba ‘ya’yanki isasshen lokaci don ki rika zama da su ta yadda za a sai-saita tunaninsu a kan rayuwa. Bai wa juna isasshen lokaci don tattauna matsalar da ta taso, zai sanya a warware matsalar cikin sauki.

Su kuma ‘yan mata akwai wasu abubuwan da ya kamata su yi a zaman gida, misali:
Sanya Sutura: Ba dai-dai ba ne ki rika sanya kaya matsattsu da ke fito da surar jikinki, alhali kin san mutane daban-daban suna shigowa gidanku. Ki yi kokarin kauce wa abin da bai shafe ki ba, musamman katsalandan a cikin zamantakewar auren ‘yangidanku, ko zuga da za ta iya haifar da husuma ko sabani a tsakaninsu.

Ki yi kokarin zama da kowa lafiya a gidanku har zuwa lokacin da ke ma za ki tafi zuwa naki gidan auren.

Hakika a gida ne a kan samu ingantacciyar tarbiyya da take bibiyar mutum har zuwa girmansa, kun ga ke nan mace tana da muhimmiyar rawar da za ta taka wajen gina nagartacciyar al’umma da za a yi alfahari da ita a duniya da gobe kiyama. Akwai bukatar mazaje su kara himma wajen inganta rayuwar a cikin gida, don a gudu tare a tsira tare.

©leadershipayau

Post a Comment

 
Top