Kamfani: Mai Shadda Inbestment da Alrahuz Film Production
Shiryawa: Ali Worth Me
Umarni: Sadik N. Mafiya
Jarumai: Aminu Shariff Momo, Falalu A. Dorayi, Sulaiman Bosho, Rabi’u Rikadawa, Abubakar Dan Auta, Baballe Hayatu, Musa Mai Sana’a, Rabi’u Daushe, Jamila Umar Nagudu, Fatima Kokobi, Fati Abubakar Shu’uma, Iliyasu Abdulmumini Tantiri, Alasan Kwalle, Aliyu Rara, Tijjani Asase. Da sauran su.
Sharhi: Hamza Gambo Umar
A farkon fim din an nuna (Fatima Kokobi) ta fito tsakar gida sai ta tarar da akuyar ta a daure, kuma an saka kwado an kulle da makulli, kasan cewar ta kurma sai ta tambayi mahaifiyar ta (Binta Kofar Soro) don jin wanda ya daure mata akuya, amma itama mahaifiyar ta wadda itama kurmar ce, sai ta nuna bata san wanda ya daure akuyar ba, adaidai sannan ne mahaifin yarinyar wato Subullu (Abubakar Dan Auta) ya fito daga cikin bandaki gami da nuna mata ya san wanda ya daure akuyar, a sannan suka dunguma suka nufi wajen Haladu (Falalu A. Doray) wanda ya nuna shi ya daure akuyar saboda idan an saketa tana yawo a gari tana yiwa jama’a barna, anan dai Subullu ya nuna lallai sai an saki akuyar don farantawa ‘yar ta sa rai.
Daga nan ne kuma aka nuna Huwaila (Fati Shu’uma) t agama kwalliya a cikin gidan su za ta dauki tallan goro da sigari, a sannan yayan ta makaho ( Sulaiman Bosho) ya shigo suka soma hira shi da mahaifiyar sa Subulluwa (Jamila Nagudu) suka nuna kushen sana’ar da Huwaila take yi saboda karuwai ne ke tallan goro da sigari, hakan yasa Huwaila da yayan ta makaho (Sulaiman Bosho) suka fara sa’insa, ganin haka ne yasa yayan nata ya dauki kyautar kudi ya bata don su daina rigimar saboda sanin cewa akan kudi za ta iya yin komai. Wata rana (Aminu Shariff Momo) yayi sallama da matar sa ya fita wajen aiki, sai wani barawo (Musa Mai Sana’a) ya nufo gidan sa don yin sata, zuwan sa ne sai ya tarar da kwarto yaje kwartanci wajen matar gidan, barawon ya labe jin tattaunawar da kwarton suke yi da matar gidan sai ga mijin ta ya dawo gida ya hango sa a jikin Katanga, hakan ne yasa ya nufo sa don ya kama sa, saidai kafin ya iso wajen ne kurma ‘yar subullu ta biyo akuyar ta cikin gidan da gudu da nufin kama ta, jin guje-gujen akuyar da kurmar ne yasa kwarto (Rabi’u Daushe) suka fito daga cikin daki a guje shi da matar gidan, wanda hakan kuma sai ya firgita barawon suka fice daga gidan a sanda me gidan (Aminu Sharif) yabi bayan su da nufin ya kama su gaba daya. A wannan lokacin ne kuma me unguwa (Aliyu Rara) ya tsiro da dokar kara haraji a cikin kauyen, yayin da ‘yan fadar sa su (Tijjani Asase) suka goyi da bayan sa, sannan suka dauke sa a kafadar su kasan cewar sa guntu suka nufi cikin gari das hi da nufin sanar da dokar sat a karin haraji, a sannan ne Haladu (Falalu A. Dorayi) ya taho da gudu akan abin hawa ya buge me unguwa ya baje a kasa, ganin hakan ne yasa ‘yan fadar sa suka bi bayan Haladu da nufin kama sa, suna cikin gudu ne Haladu ya hadadu da kwarto da barawo (Musa Mai Sana’a) da (Rabi’u Daushe) wadanda (Aminu Shariff) ya biyo su saboda sun shiga gidan sa yin kwartanci, haduwar su ne yasa suka gudu gaba daya suka buya a cikin wata bukka har sai bayan wadanda suka biyo su sun tafi sannan suka fito suka sake guduwa, a sannan ne ‘yan fadar me unguwa suka kama Haladu suka nufi wajen me unguwa da su. Yayin da su kuma barawo da kwarton da (Aminu Sharif) ya biyo suka buge su Jatau (Rabi’u Rikadawa) wanda ya zauna suke caca da abokan sa.
Ganin an buge su ne suka tsorata duk suka arce a guje, duk suka nufi gidan kwarto (Rabi’u Daushe) shigar su cikin gidan ne har suka buge dan (Rabi’u Daushe) yaron ya karye, yayin da (Aminu Shariff) ya kama su, kuma iyalan kwarton bayan sun ji abinda mijin su ya aikata suka yi tur da halin sa. A bangaren Jatau (Rabi’u Rikadawa) sai ya shawarci matar sad a nufin su dauki da gidan su da suke zaune a ciki gami da gidan yayan ta Subullu (Abubakar dan Auta) da nufin a su saka gidajen a caca don su cinye ainahin gidan abokan sa wanda su ma za su saka gidajen a caca. Jin hakan sai ta amince kuma shima yayan ta Subullu ya amince da hakan suka dauki gidajen suka saka a cikin caca.
Fim din ya nishadantar kuma ya ja hankalin masu kallo, sai dai kuma babu wani muhimmin darasi wanda kai tsaye mai kallo zai karu dashi, domin an nuna abubuwa na rashin tarbiyya wadan da jama’a suke aikatawa, amma ba’a bayyana hanyoyin gyaran su ba, sannan kuma labarin bai dire har karshe ba, domin akwai abubuwan da ba a kammala tare da karkare su ba. Wallahu a’alamu!
Sources:Leadershipayau
Post a Comment
Click to see the code!
To insert emoticon you must added at least one space before the code.