Hukumar NSCDC na jihar Ondo ta gabara wa manema labarai wani saurayi mai suna Ebuka Okafor mai shekar 20 wanda ta ce ya aikata luwadi da wasu kananan yara guda biyu a birnin Akure. Majiyar isyaku.com ta ce an cafke Ebuka ne yayin da yake kokarin aikata luwadi da daya yaron a unguwar Oja-Oshodi da ke birnin Akure kafin dubu ta cika, kuma aka likida mashi dan karen duka har ya suma kafin daga bisani aka kai shi fadar mai gari inda shi kuma ya bayar da umurnin cewa a mika shi ga rundunar NSCDC.

Kwamandan rundunar NSCDC na jihar Ondo Pedro Awili, ya tabbatar wa manema labarai da faruwar lamarin, ya ce sauran kadan jama'ar unguwa su halaka shi kafin a ja shi zuwa fadar Deji na unguwar inda shi kuma ya aika mai laifin zuwa ofishin NSCDC domin a gudanar da cikakken bincike.

Ebuka Okafor ya tabbatar wa manema labarai cewa ya sha aikata luwadi tare da wadannan yara yan shekara 12 da 13, kuma yakan basu N200 a ko da yaushe ya yi lalata da su tun wata biyu da suka gabata.

DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafin mu na Facebook facebook.com/isyakuweb

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0

Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

WAYAR KA TA LALACE KO KANA BUKATAR FLASHING? 

Garzaya zuwa SENIORA TECH,shago mai lamba 50, hawa na sama gefen hagu,TAUSHI PLAZA , yamma daga gidan marigayi Waziri Umaru,kan Tiltin Ahmadu Bello, Nassarawa, Birnin kebbi jihar Kebbi. Barka da zuwa gidan sauki wajen gyaran wayar salula a garin Birnin kebbi.

Post a Comment

 
Top