Wata jaruma ma'abuciya nuna tsiraici domin kawa ta sha tofin Allah tsine a intanet bayan ta bude al'aurarta a cikin wani Masaallacin Marisa Papen da ke kasar Turkiyya yayin da take sanye da Burka kamar yadda majiyar isyaku.com ta shaida mana.

Majiyar isyaku.com har ila yau, ta shaida mana cewa wannan budurwa Marisa Papen ta sha banbaro rigima ta hanyar tubewa zindir a warare masu tsarki na ibada a can baya,majiyar ta ce an taba daure Marisa Papen a Kurkuku bayan ta tube zindir ta dauki hotuna a cikin wani wurin ibada na Karnak kusa da birnin Luxor a kasar Masar watau Egypt.

Hakazalika ta taba daukan hoto tsirara a wani waje da ke nuna bangon Wailing daga kasa, daya daga cikin wurare masu tsarki ga mabiya addinin Yahudawa na Judaism a birnin Kudus watau Jerusalem da ke kasar Isra'ila.

DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafin mu na Facebook facebook.com/isyakuweb

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0

Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com

Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

WAYAR KA TA LALACE KO KANA BUKATAR FLASHING? 

Garzaya zuwa SENIORA TECH,shago mai lamba 50, hawa na sama gefen hagu,TAUSHI PLAZA , yamma daga gidan marigayi Waziri Umaru,kan Tiltin Ahmadu Bello, Nassarawa, Birnin kebbi jihar Kebbi. Barka da zuwa gidan sauki wajen gyaran wayar salula a garin Birnin kebbi.

Post a Comment

 
Top