Daga Wakilinmu

Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC ta bayyana cewa ikon da hukumar ta sa ke da shi bai kai karfin tambaya ko bincikar inda takardun shaidar karatun ‘yan takarar zaben 2019 suke ba.

Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka da kan sa, jiya Juma’a, a lokacin da ya ke amsa tambayoyin manema labarai a Abuja, a kan batun ‘yan takarar da aka lika sunayen su.

Ya ce abin da INEC ta yi shi ne buga sunayen ‘yan takarar tare da likawa a allo kowa ya gani da idon sa, kamar yadda doka ta umarci hukumar ta yi kwanaki bakwai bayan kammala damka mata sunayen.

Batun ya taso ne bayan da aka ga cewa Shugaba Muhammadu Buhari bai hada wa INEC da takardun shaidar jarabawar kammala sakandare ba, wato WAEC.
Maimakon haka, Buhari ya sake jaddada wa INEC abin da ya shaida musu a lokacin da ya cika fam na takarar zaben 2015 cewa takardun sa har ila yau, su na a hannun hukumomin tsaro na soja.

Buhari ya yi wannan jaddadawa ce ta hanyar yin rubutacciyar rantsuwa da kwansitushin a kotu, wato ‘affidavid’.

Yakubu ya ce abin da dokar kasa ta ce INEC ta yi, shi ne bayyana bayanan kowane dan takara, kuma ta yi kowa ya gani. Amma batun binciken takardun bayanan kowane dan takara, ba aikin INEC ba ne.

Ya ce wannan hakkin jama’a ne ‘yan Najeriya, su tashi tsaye su nemi sani ko ganin cikakkun takardun kowane dan takara, idan har ta kama mutum ya bi ba’asin maganar a kotu, zai ma iya garzayawa domin ganin kwakwaf. Inji Yakubu.

Shugaban na INEC ya ce dokar INEC ta ce kowane dan takarar shugaban kasa, zai cika fam na CF001, tare da hado mata shi da rantsuwa daga Babbar Kotun Tarayya, Babbar Kotun Jiha ko ta Babban Birnin Tarayya, cewa bayanan da ke cikin fam din na sa ne, kuma haka su ke.

Ya kara da cewa kuma kamar yadda INEC ta lika sunayen ‘yan takarar shugaban kasa, haka za ta lika sunayen ‘yan takarar gwamna a ranar 2 Ga Nuwamba, 2018.

 “Kun ga wannan wata dama ce ga ‘yan Najeriya su binciki bayanan da kowane dan takara ya mika wa INEC. Idan akwai inda wani ke ganin cewa dan takara ya bayar da bayanai ba daidai ba, ya na da ‘yancin garzayawa kotu ya maka shi kara. Saboda ita INEC komai na ta a sarari ya ke, babu nuku-nuku.”

Yakubu a tabbatar da cewa jam’iyyu 79 ne za su shiga takarar shugabancin kasa daga cikin 89 da suka shiga zabe.

Akwai ‘yan takarar sanata 1803 da ke neman nasarar hawa kujerun sanata 109 na Majalisar Dattawa.
Sannan kuma akwai ‘yan takarar Majalisar Tarayya 4,548 masu neman yin nasara a kan kujerun majalisar tarayya 360 na fadin kasar nan.

Za a yi zaben gwamna a jihohi 29, sannan ya kara da cewa jihar Zamfara ba ta damka wa INEC sunan dan takarar gwamnan ta ban a APC, kamar yadda jam’iyyar ta yi ikirari.

Post a Comment

 
Top