Matakin sassauta dokar ya biyo bayan zaman da kwamitin Tsaro na gwamnatin Jihar yayi ne a yau talata.
Sanarwa ta Bayyana cewar an sassauta dokar a yankin kasuwar magani da Kujama inda jama'a za su iya gudanarwa da harkokin su daga karfe shidda na safe zuwa Biyar na yamma har abinda hali yayi.
Amma har yanzu Dokar fita ta awa 24 na cigaba a yankunan Kabalan Doki , Sabon Tasha, Narayi da maraban Rido dake cikin garin Kaduna,inda aka samu tashin Hankali sosai sakamakon kai farmaki a wuraren ibadu daban daban.
Yayin da sauran sassan garin Kaduna kuwa an takaita dokar Mutane na iya fita tun da misalin karfe daya na ranar yau har ya zuwa Biyar na yamma, za a bude kasuwanni da shaguna kuma jami'an tsaro za su cigaba da sintiri a cikn gari domin Tabbatar da doka da Tsaro.
Sanarwa daga Samuel Aruwan mai magana da yawun gwamnatin Jihar Kaduna.
Post a Comment