Suna: Karshen Wata Riga
Tsara Labari: Nasir S. Gwangwazo
Kamfani: Halifa Abubakar Inbestment
Shiryawa: Halifa Abubakar Kafar Wambai
Umarni: Ali Gumzak
Jarumai: Sadik Sani Sadik, Rabi’u Rikadawa, Baba Hasin, Nasir Naba, Hajara Usman, Hasana Muhammad, Shu’aibu Yawale, Khalisat Mamza. Da sauran su.
A fim din an nuna Magaji (Ali Nuhu) yazo gidan Baffa Manu (Rabi’u Rikadawa) tare da jami’an tsaro da kuma su Joda (Hafsa Idris) da mahaifiyar ta, inda jami’an tsaro suka nunawa Baffa Manu wani guru suka tambayesa abinda ya sani akai, anan ya fara nuna bai san komai ba, amma ganin jami’an tsaron sun yi masa jan ido suna son jin gaskiyar lamari, sai ya fada musu cewar gurun kanin sa ne kuma tabbas shi ya kashe kanin nasa wato Ardo Salihi (Sani Garba S.K) jin hakan ne yasa mahaifiyar Joda ta soma la’antar sa gami da nuna takaicin ta akan yadda son kudi ya sanya shi kashe mijinta kuma kanin sa wanda suka fito ciki daya. Nan fa jami’an tsaro suka cafke Baffa Manu suka sanya shi a motar su don zuwa ofishin su. Bayan an tafi dashi ne Joda take tambayar Magaji inda maganar auren su ta kwana, amma sai ya nuna ta kwantar da hankalin ta zai aure ta.
A wani bangare kuwa cikin wani sashen fulanin daban an nuna Adda (Hajara Usman) tare da mijinta (Baba Hasin) da ‘yar su Meroji (Hassana Muhammad) suna tattauna damuwar su akan tafiyar da zasuyi zuwa wata rugar ta daban, sai dai kuma ba sa so suyi tafiyar su bar ‘yar su da take aure a hannun manoma, sun yi tunanin yadda zasu kubutar da ita saboda suna ganin cewar idan wata fitina ta taso mijin ‘yar tasu bazai iya kubutar da ita ba. Haka itama ‘yar ta su Fatu (Khalisat Mamza) a can garin manoma da take aure kullum tana cikin damuwa saboda samun labarin cewar iyayen ta za su yi kaura su koma wata rugar, tana ganin idan sun tafi kamar ba za su sake haduwa ba, jin hakan yakan sa mijinta Amadu (Sadik Sani Sadik) ya rarrashe ta gami da nuna mata cewar ko babu iyayen ta shine gatan ta. Kwatsam ana tsaka da haka sai aka sako Baffa Manu daga hannun jami’an tsaro a sanadiyyar ‘yan siyasar da yake mu’amula dasu wadanda suka goya masa baya, bayan dawowar sa ne suka hadu da mahaifin Meroji wanda yake tunanin hanyar da zai ceto ‘yar sa Fatu daga hannun manoma don su yi kaura daga cikin rugar tare da ita. Daga bisani suka yanke shawarar zuwa garin manoma don tahowa da ‘yar su Fatu saboda suna ganin cewar yin hakan shine kadai mafita. Haka itama Fatu a koda yaushe tana cikin zullumin zamanta a garin manoma domin gani take kamar za su iya kawo mata darmakin bazata, hakan yasa daga taji kwakwkwaran motsi sai ta firgita ko da kuwa mijinta Amadu ne ya taho ba tare da ta sani ba, ganin halin da take ciki ne yasa mijinta Amadu yake kara rarrashin ta gami da nuna mata cewar babu mahalukin da zai shigo har gida ya illata ta. A bangaren manoma kuwa duk suna cike da takaicin ganin dan uwan su Amadu ya auro ‘yar makiyaya kuma ya ajiye ta a cikin garin su, hakan yasa suka soma tunanin hanyar da za su kashe ta saboda su rama abinda makiyaya suka yi musu wajen kashe musu dangin su. Manoman sun zauna shawarwarin irin matakin da za su dauka akan Fatu wanda daga karshe bayan sun tattauna da dattijan kauyen su sai suka yanke shawarar cewar su kashe Fatu, kuma sun ci alwashi cewar idan mijinta Amadu yayi kokarin hana su ko wata gardamar daban to za su hada har shi su kashe sa, da wannan shawarar suka yi amfani suka soma shirin kashe Fatu don fitar da ahlin makiyaya daga cikin su. Yayin da a can bangaren iyayen Fatu kuwa sun gama yanke hukuncin zuwa garin da take aure don su dauko ta, bayan sun gama shirye-shirye ne sai Mairoji (Hassana Muhammad) tayi sallama da saurayin ta Musa (Nasir Naba) wanda yake ganin sam bai kamata masoyiyar tashi ta tafi ta bar shi ba, amma sai ta nuna masa tafiyar tasu ta zama dole, haka ya hakura ya kyaleta suka yi sallama irin ta masoya cike da kewar juna. Cikin dan lokaci kadan su Mairoji da iyayen ta suka kama hanyar tafiya, yayin da tun a hanya Mairoji take fadawa iyayen ta cewar tanaji a jikin ta kamar ba zata dawo ba, haka shima saurayin ta Musa bayan tafiyar ta sai ya kasa nutsuwa, shima yayi sallama da mahaifiyar sa yabi bayan masoyiyar sa. Ita kuwa Fatu kurum babu zato matasan gari suka shiga gidan da mugayen makamai suna kokarin halaka ta, a sanda suke shirin balla kofar dakin ta ne mijinta Amadu ya shigo gidan suka soma gardama da matasan kauyen, har sun soma kokarin yi masa illa sai mahaifin Amadu ya shigo gidan yayiwa matasan dadin baki suka fice daga gidan. Daga nan ne Amadu sa mahaifin sa suka sanar da mai unguwa halin da ake ciki yayin da shi kuma ya nuna zai fadawa hakimi don a dauki mataki. Tsakar dare iyayen Fatu suka iso cikin garin suka bukaci tafiya rugar su da ita, amma sai Amadu ya nuna rashin amincewar sa, suna cikin tattaunawa mutanen kauyen suka shigo suka yi yunkurin halaka Fatu da iyayen ta gaba daya, daya daga cikin matasan yayi kokarin kai was Fatu duka da makami sai kanwar ta Mairoji ta kare dukan, anan fa ta fadi kasa ta mutu, ganin hakan yasa manoman suka fice daga gidan, yayin da su kuma iyayen Fatu gaba dada suka soma alhinin rashin ‘yar su, babu zato sai Musa saurayin Mairoji ya shigo gidan, ganin an kashe budurwar sa Mairoji ne hakan ya sanya shi cin alwashin daukar matakin fansa akan manoma.

Abubuwan Birgewa:

1- Labarin ya tafi kai tsaye zuwa ga sakon da ake son isar wa, haka kuma labarin ya taba zuciya musamman lokacin mutuwar Mairoji.
2- An samar da wuraren da suka dace da labarin.
3- Wakar fim din tayi dadi kuma tana dauke da sakon fadakarwa.
4- Camera ta fita radau, sauti ma ba laifi.

Kurakurai:

1- Lokacin da jami’an tsaro suka zo kama Baffa Manu (Rabi’u Rikadawa) bai kamata su tuhumeshi a kofar gidan sa da nufin sai ya amsa musu laifin kisan da ake zargin sa dashi ba. Ya kamata ace sun kai shi can ofishin su sannan su tuhumeshi don jin gaskiyar kashe kanin sa da yayi.
2- An nuna wasu ‘yan siyasa sun kebe tare da wani matashi da nufin siyan shanu masu yawa a wajen sa, sai dai kuma har fim din ya kare me kallo bai ga dalilin da yasa ‘yan siyasar suka shirya siyan shanun makiyayan ba.
3- Bayan jami’an tsaro sun kama Baffa Manu (Rabi’u Rikadawa) daga bisani kuma sai mai kallo ya gan sa ya dawo a bisa cewar da aka yi ‘yan siyasa sun fitar dashi. Shin Baffa Manu ya kashe kanin sa a bulus kenan? Tunda ba’a nuna yayi nadama ba, ya dace a nuna wani alhakin na hakkin rai yana bibiyar sa don hakan ya zamo izina ga masu irin halin sa.
4- An shigo da ‘yan siyasa a bangaren Fulani, sai dai kuma har fim din ya kare me kallo bai ga amfanin su a labarin ba, ya dace a bayyanar da dalilin sanya su a labarin ko da ta hanyar nunawa matasa illar bangar siyasa ne ko kuma wani amfanin ‘yan siyasar a cikin irin kauyukan.
5- Shin su Joda (Hafsa Idris) sun yi kaura sun canja gari ne? Tun bayan jami’an tsaro da suka kama Baffa Manu (Rabi’u Rikadawa) me kallo bai sake ganin Joda da mahaifiyar ta ba, haka shima Magaji ba’a sake ganin sa ba duk da ba’a bayyana cewar yayi wata tafiyar ko kuma ya auri Joda sun bar garin ba.
6- Shin mecece alakar Baffa Manu da mijin ta Adda (Hajara Usman)? Ya kamata a bayyana alakar dake tsakanin su.
7- Rugar da aka cigaba da ganin Baffa Manu (Rabi’u Rikadawa) batayi kama da Rugar fulanin da aka gan sa a baya ba, haka kuma mutanen da aka saba gani a waccan rugar tsirarun su ne a wannan rugar, jama’ar sun sha bamban da wadanda aka nuna a wannan muhallin, idan kuma sun sake komawa wata rugar ne kamar yadda aka nuna a baya, to ya dace a yiwa me kallo bayani ko da baki ne.
8- Dukkan manoman da aka nuna a wancan fim din na farko wato (Wata Ruga) wadanda aka kashewa dangi, ba su aka sake nuna wa ba a wannan fim din. Ya dace a bayyana dalilin hakan ko don a wayar da kan me kallo.

Karkarewa:

Fim din ya fadakar domin ya tabo matsalolin da suke ta faruwa a tsakanin manoma da makiyaya, musamman irin matsalolin dake afkuwa na rashin kwanciyar hankali bayan auratayya ta shiga tsakanin manoma da makiyaya. Sai dai kuma labarin ya sauya salo ta yadda wasu ba za su fahimci cewar ci gaban Wata Ruga bane, ya dace Magaji (Ali Nuhu) ya zamo shine a madadin Amadu (Sadik Sani) haka kuma Joda (Hafsa Idris) ta zamo a matsayin Fatu (Khalisat) domin kuwa Magaji da Joda ne aka nuna a matsayin ‘ya’yan Manoma da Makiyaya masu son auren juna, fim din sai yafi zama daidai a zukatan masu kallo idan aka bar Magaji da Joda a gurbin su Amadu. Wallahu a’alamu!

Post a Comment

 
Top