- An samu daidaito da gwamnati akan matsalar da aka samu da Mtn

- Bankin kasa tare da MTN suna aiki kafada da kafada don samun daidaito akan lamarin - Muna kokari don ganin hakan bai sake faruwa ba a nan gaba.

Zainab Ahmed tace gwamnatin tarayya ta samu daidaito dangane da masu zuba hannun jari dake kasashen ketare wanda MTN ya shiga tsakani. Da take magana a ranar Talata a Abuja tace bankin kasa tare da kamfanin na MTN suna aiki kafada da kafada don kawo karshen matsalar.

Tace "Abinda ya faru da MTN yayi mana illa matuka,wannan dalili yasa muka fara bincike akai".

Amma akwai wasu kasuwancin daya kamata gwamnati ta dunga sanya dokoki akai.

 Bayan faruwar wannan lamari CBN ya tattara duk wani bayanai daya kamata a cikin watanni Biyu zuwa yanzu an kawo karshen matsalar. Ahmed ta tabbatar wa da masu zuba hannun jari cewa babu wani kamfani dazaifi MTN. CBN ya umarci MTN da wasu bankuna hudu dasu dawo da kudi wanda yawansu yakai $8 billion.

Post a Comment

 
Top