Jakar magori na isyaku.com ya leka garin Azua a kasar Dominican Republic, inda ya samo mana labarin wani matashi da ya sha guba ya halaka kanshi domin budurwarsa ta aika masa wani hoton bidiyo da ya nuna yadda take soyayya da wani.

Majiyarmu ta ce jim kadan bayan ganin wannan bidiyo da ya nuna budurwarsa tana rungume-rungume da wani saurayi dabaan, sai gogan naka ya kasa jurewa, ya samo guba ya kwankwade, daga bisani kuma ya galabaita.

Sakamakon haka aka garzaya da shi zuwa wani Asibiti inda ya ce ga garinku. Mutuwarsa ya jefa jama'ar garin Azua cikin matukar mamakin ganin yadda wannan budurwa ta yi sanadin mutuwar saurayin nata da gangan ta hanyar aika masa hotunan bidiyon.

Wata majiya ta ce budurwar ta yi haka ne domin ta harzuka shi bayan sun sami wata yar matsala, amma sai zakin kidi  ya sa kalangu ya fashe, domin dai wannan saurayi ya bar ma budurwarsa Duniyar ce gabadaya.


DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafin mu na Facebook facebook.com/isyakuweb

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0

Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

WAYAR KA TA LALACE KO KANA BUKATAR FLASHING? 

Garzaya zuwa SENIORA TECH,shago mai lamba 50, hawa na sama gefen hagu,TAUSHI PLAZA , yamma daga gidan marigayi Waziri Umaru,kan Tiltin Ahmadu Bello, Nassarawa, Birnin kebbi jihar Kebbi. Barka da zuwa gidan sauki wajen gyaran wayar salula a garin Birnin kebbi.

Copyright, do not copy and paste our news on your blog without expressed  permission from us.

Post a Comment

 
Top