A ranar Talata ne Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewar tana kan gabatar da wani kwakkwaran aiki domin fitowa da wani tsari da zai kayyade yawan yaran da kowacce uwa za ta haifa a Nijeriya.

Ta bayyana cewar ta soma shigo da shuwagabannin gargajiya da sauran shuwagabannin al'umma na gaba daya fadin kasar nan cikin lamarin. Gwamnatin ta bayyana cewa ta dauki aniyar hakan domin shawo kan daya daga cikin manyan matsalolin da ke hana farfadowar tattalin arzikin kasa da kuma tsare-tsaren gwamnatin tarayya na bunkasa kasa.

Ministar kudi, Zainab Ahmad, wadda ta bayyana hakan yayin da take bayar da amsar wata tambaya da aka mata a gurin wani taro kan tattalin arzikin Nijeriya da aka gabatar a Habuja, ta bayyana cewar yawan al'ummar kasar na daya daga cikin manyan abubuwan da ke kawo tsaiko ga cigaban kasa.

Post a Comment

 
Top