Mun samu labari cewa masu takarar Shugaban kasa a Najeriya sun kulla damara inda su ka mika takardun su gaban Hukumar zabe na kasa watau INEC. Shi dai tuni Atiku Abubakar na PDP ya mika duk abin da ake bukata.

‘Dan takaran Shugaban kasan na PDP Atiku Abubakar ya gabatar da takardun karatun sa na Boko wanda su ka nuna cewa yayi Difloma a Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya. Atiku ya karantar ilmin harkar shari’a ne a shekarar 1969.

Har wa yau, Atiku ya bayyanawa Hukumar zabe cewa daga 2015 zuwa 2018 ya samu kudi Naira Miliyan 60.2. Daga cikin wannan kudi ‘Dan takaran ya biya Najeriya harajin sama da Naira Miliyan 10 kamar yadda doke tace.

Jaridar Punch ta rahoto cewa shi kuma Shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda yake neman zarcewa a kan karagar mulki a APC ya bayyanawa Hukumar zabe na Kasa watau INEC cewa takardun sa duk su na gidan Soja.

A lokacin zaben 2015 ma dai Shugaba Muhammadu Buhari bai bada takardun sa ba inda sai dai ya cike takardun rantsuwa ya tabbatar da cewa takardun na sa su na wajen Sakataren gidan Sojin Najeriya.

Post a Comment

 
Top