Daga Maje El-Hajeej Hotoro
1. Daga cikin Hanyoyi mafi muni na cin dukiyar Haram mafi muni shine karbar cin hanci da rashawa. Wanda Aka Tsinewa Mai Bayarwa Aka Kuma Tsinewa Mai Karba. Abdullahi bn Amr (Allah Ya kara yarda da shi) ya ruwaito daga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam cewa, " Allah Ya la'anci mai bayar da cin hanci da kuma mai karba.
2. Juya gaskiya ta koma karya ko kuma juya karya ta gaskiya kamar yadda alkali da lauyoyi ke yi na daga rashawa mai muni. Alkali a ba shi rashawa ya kwace gaskiya daga wajen mai gaskiya ya ba wa makaryaci. Ko Jami'an tsaro a ba su rashawa su juya laifi daga mai laifi su mayar kan mara laifi.
3. Kamar yadda wani ya kira ni a waya yana Tambaya ta ya taba aikata wani laifi da yake damunsa. Sun taba kama 'yan fashi guda biyar wadanda aka yankewa hukuncin kisa, sai daya daga cikinsu ya ce yana da kudi masu yawa a boye idan suka sake shi zai ba su. Suka tafi hanyar kauye suka samu wani bawan Allah da bai san hawa ba bai san sauka ba suka yi masa duka sannan suka sa shi a cikin barayin aka je aka kashe shi.
Daya daga cikin wadannan Jami'an tsaro ya bar aiki shekaru da dama, amma duk sanda ya kwanta barci sai ya rika hango wannan mutumin.
4. Kowa ya san halin da ake ciki a Kano wanda duniya gabadaya kallo ya dawo kan Kano. Sakamakon tuhuma da ake yi wa mai girma Gwamna na karbar cin hanci da rashawa daga hannun 'yan kwangila. Wanda wasu bidiyo ke ta yawo a kafafen yada Labarai, kuma majalisar dokokin jihar Kano tana bincike domin gano gaskiya ko karyar wannan bidiyon.
5. Wannan abu da Majalisar ta yi abu ne mai kyau domin tabbatar da gaskiya da kuma yin aiki da ita. Domin mutane ne guda biyu, daya dan jarida daya dan siyasa.
6. Dan jaridar nan daga yada bidiyon nan ya saba Alkur'ani ya zo Majalisar ya tabbatar da cewa wadannan bidiyon gaskiya ne. Sannan a bangaren gwamnatin sun ce wadannan bidiyon karya ne, kage ne, sharri ake wa mai girma Gwamna.
7. To yanzu ina gaskiya ta ke? Idan ka ce karya da kage da sharri aka yi wa maigirma Gwamna da wanne dalili? Idan ka ce gaskiya ne mai girma Gwamna yayi haka da wanne dalili? Wa za ka gasgata a cikin wadannan bangarori guda biyu?
8. Wannan ne ya sa Kasashen duniya suka zuba ido ga majalisar domin tabbatar da gaskiyar dan jarida ko karyar sa. Ko kuma tabbatar da gaskiyar Gwamna ko karyar sa.
Wanda a karshe kowanne ne ya faru darasi ne a garemu Al'umma gabadaya.
9. Idan ya tabbata karya da kage da sharri aka yi wa maigirma Gwamna wannan zai Kara masa kima, zai kara masa mutunci zai kuma kara masa daraja.
Sannan kuma zai zama hukunci mai tsanani akan Dan jaridan da ya yi yunkurin bata masa suna.
10. Idan kuma ya tabbata wannan kudi na rashawa ne mai girma Gwamna ya karba wannan zai zama babban kamu a jihar Kano wanda ba a taba yin irin sa ba. Shine kama dan siyasa mafi girma a jihar Kano, kuma idan an hukunta shi wannan zai zama babban darasi a kasa baki daya.
11. Musamman Gwamnantin da shugaba Buhari yake jagoranta wacce ya shelantawa duniya zai yaki cin hanci da rashawa da tabbatar da tsaro. Wadannan sune Abubuwan da ya yi kamfen da su a shekara ta 2003 da shekara ta 2007 da shekara ta 2011 da shekara ta 2015 da kuma shekara ta 2019 da yanzu za a shiga zabe.
Abin dai bai canja ba shine yaki da cin hanci da rashawa da farfado da tattalin arziki da kuma tsaro.
12. Idan wannan abu ya tabbata aka yi kokarin canja shi ko aka yi kokarin murde shi wannan zai zubar da mutuncin jihar Kano dama kasa baki daya. Sannan zai nuna cewa yaki da cin hanci da rashawa da ake cewa ana yi ba gaskiya ba ne.
13. Akan wannan an daure manyan 'yansanda. Akan irin wannan tuhuma an cire babban jami'in DSS. Akan Irin wannan tuhumar an kama Malam Ibrahim Shekarau wanda yayi Gwamnan jihar Kano shekara takwas, yayi Minista kuma Basarake ne. Duk da mutuncinsa da darajarsa da kimarsa da ake gani a jihar Kano an kama shi an kai shi kotu ana tuhumar sa da cin kudi na rashin gaskiya.
14. Ka ga wannan idan Gwamnati ta dauki mataki na tabbatarwa ko kuma korewa wannan zai zama babban darasi ga 'yan siyasa. Nan gaba za a ce da Dan siyasa ga mulki ya ce ba ya so saboda ya ga ana hukunta manya. Sannan rigima da zubar da jini gami da shaye-shaye za su ragu akan son mulki. Saboda mutane za su ga ko ina ka je ba za ka sha ba idan aka same ka da cin dukiyar Al'umma.
Post a Comment