A jiya Alhamis, 18 ga watan Oktoba 2018 wasu daga cikin jaruman Finafinan Hausa da mawaka suka kai ziyara ta musamman a fadar shugaban kasa Nijeriya Muhammad Buhari. Sai dai da alama ziyarar ta su ta bar baya da kura saboda irin yadda aka rika ce-ce-ku-ce game da ziyarar, ya yin da wasu ke ganin cewa an ware su tafiyar. Akwai ma wasu wadanda suka bayyana cewa su ba su san da tafiyar sai dai kawai suka ga hotuna a soshiya midiya amma kuma an bayyanawa shugaban kasa duk 'yan Kannywood suna goyon bayan sa.
Wata Majiya ta tabbatar mana da cewa duk 'yan fim da mawaka da suka halarci wurin sai da aka ba kowa Naira Dubu 250, a gefe guda kuma wasu suka ce akwai wadanda dubu 10 ma suka samu a tafiyar, Tuni dai an ce wasu daga cikin su suna can sun kama hotel a Abuja, za su ci wani abu daga kudin. Bugu da kari wasu daga cikin 'yan fim da mawaka na Jihar Katsina sun yi wa ziyarar tofin Allah tsine! A cewar su duk wanda ya yi magana da yawun su Allah ya isa ba su yafe ba domin an maida su saniyar ware.
Wani Daraktan Finafinan Hausa da ba a yi tafiyar da shi ba, yana shirin kwance masu zane a kasuwa nan bada dadewa ba, a cewar sa taron maroka ne da 'yan maula, a gefe guda kuma wata majiya ta tabbatar mana da cewa akwai wani jarumi dan Jos da ya tada rigima a Hotel kafin a raba kudi.
Sannan akwai wasu daga cikin jaruman Finafinan Hausa da su ka ce, za su fito su bayyanawa duniya cewa su ba tafiyar Buhari suke yi ba, wadanda suka je jiya kawai sun ari bakinsu ne sun ci masu albasa.
Ku biyomu zuwa gobe domin jin cikakken labarin ziyarar.
© KANNYWOOD EXCLUSIVE
18-10-2018.
Post a Comment