Tsohon gwamnan jihar Yobe, Bukar Abba Ibrahim, ya bayyana cewar zai yi wuya jam'iyyar APC ta iya yin nasara a zaben shekarar 2019 ko da za ta yi magudin zabe.

Bukar Abba, sanatan APC mai wakiltar gabashin jihar Yobe ya ce al'amura sun kara lalacewa karkashin mulkin jam'iyyar APC tare da bayyana cewar matukar ba su gaggauta yin gyara ba za su sha kaye a zaben 2019.

Kazalika ya bayyana cewar bai kamata a raina yankin arewa maso gabas ba, yana mai fadin cewar mutanen yankin sun san 'yancin su a siyasance.

"Babu abin da ya canja, lamura ma sun kara lalacewa ne kawai. Ran jama'a a bace ya ke, ba na jin ko da magudi za iya lashe zabe.

Sources: mikiya.

Post a Comment

 
Top