Rundunar yansandan jihar Kaduna ta ce kimanin mutum 55 ne aka kashe sakamakon wani fitina da tashin hankali da ya kaure tsakanin al'umman Kasuwan Magani da ke karamar hukumar Kajuru a jihar ta Kaduna ranar Alhamis. Sanarwar haka ta fito ne daga bakin Kwamishinan 'yansanda na jihar ta Kaduna Ahmad Abdul-rahman yayin da yake zantawa da manema labarai ranar Juma'a.

Kwamishinan ya ce rundunar 'yansandan jihar ta kama akalla mutum 22 dangane da wannan tashin hankali kuma jami'anta na gudanar da bincike.

Tun ranar Alhamis ne gwamnatin jihar Kaduna ta ayyana dokar ta baci na awa 24 a wannan yankin domin kawo zaman lafiya da samar da tsaro ga rayuka da dukiyar jama'ar wannan yanki.


Shiga shafin mu na Facebook facebook.com/isyakuweb Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0 Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

KANA ZAUNE A BIRNIN KEBBI? WAYAR KA TA LALACE KO KANA BUKATAR FLASHING? 

Garzaya zuwa SENIORA TECH,shago mai lamba 50, hawa na sama gefen hagu,TAUSHI PLAZA , yamma daga gidan marigayi Waziri Umaru,kan Tiltin Ahmadu Bello, Nassarawa, Birnin kebbi. Barka da zuwa gidan sauki wajen gyaran wayar salula a garin Birnin kebbi.

Post a Comment

 
Top