Jaafar Jaafar Ya Bayyana A Majalisar Jiha
Saukar Jaafar Jaafar ke da wuya a majalisar jihar Kano bai zame ko ina ba sai dakin da kwamitin tuhumarsa da aka tanada. Nan ya iske mambobin kwamitin fuskokinsu tamkar mufutin alkali. Ba tare da bata lokaciba tambayoyi kamar haka suka fara da su:

Tambaya 1: Wanene kai Jaafar Jaafar a cikin yan jaridun Najeriya.

Amsa: Nine dai Jaafar Jaafar, mai buga jaridar Daily Nigeria.

Tambaya 2: Wacce hukumace ta baka lasisin buga labarai.

Amsa: Nan ya mika masu kwafin takarda da babu wanda yasan me ta kunsa, sai mambobin.

Tambaya 3: Su wanene yan kwangilar da suka shaida maka Gwamna Ganduje na karbar rashawa daga yan kwangila.

Amsa: Baku duba dokokin kasa da suka haramtawa yan jaridu bayyana sunan masu bada labarai garemu.

Tambaya 4: Mu nan ba kasa bace, majalisar jihar Kano ce. Ka fadamana su waye.
Amsa: A’a.

Tambaya 5: Mun san yan kwangilar mu kaf. Tunda muna taka rawa kan ayyukan kwangiloli.

Amsa: Hakan yazo da sauki, sai ku gayyacesu kamar yadda kuka gayyaceni.

Tambaya 6: Ta yaya ka mallaki “video cliffs” (clip) din da kake saki, wa ya tantance maka gaskiyarsu.

Amsa: Na fada maku a baya dokar kasa ta bada kariya ga abinda ake kira ‘source’ wato masu kawo bayanai. Saannan “video cliffs” kamar yadda kuka ambacesu a takardar gayyatata sun zama mallakar kowannenku, kuna iya amfani da kwararru su tantance gaskiyarsu ko akasin haka.

Tambaya 7: Ba zaka fada mana su waye suka baka video da kuma bayarda $5m, jakan zai sanyamu kai ruwa rana da kai.

Amsa: Wadannanne tambayoyinnaku da kuka katsemin aikina, har na baro ofoshina a Abuja. Babu komai dolene mutum irina ya mutunta majalisar dokoki. Kuma kada ku manta, lokacin da na fidda zargin almundahanar kudi a masarautar Kano baku gayyaceni ba, kuka shiga aikin bincike gadan gadan.

Jaafar Jaafar: Nagode muku zan koma kan aikina a can Abuja, sai kun tanadi wasu tambayoyin ko kuma kun gayyaci duk yan kwangilar gwamnatinnan kan ko suna baiwa gwamna Ganduje rashawa.
Tashi-tashi an dawo da wutar ka koma daki. Nan na ankara mafarki nake.

Post a Comment

 
Top