Isyaku Garba - Birnin kebbi-28-10-2018
Dorewar wanzuwar zaman lafiya a kowace kasa ya dogara ne kacokam ga shuwagabannin Addini da na Al'umma.
Rev.Zakka Peter Ahuce ne ya furta hakan, wurin taron wayarda kai na wuni daya ga masu ruwa da tsaki kan sha'anin Addini, da aka gudanar a babban birnin jihar Kebbi,watau Birnin Kebbi.
Muhammad Yazeed Umar, na daga cikin mahalarta taro ga rahoton da ya aiko Mana.
Danna nan kasa ka saurari sauti 👇👇👇
Wannan taron ya sami halarcin Mukaddashin Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi Alh. Samaila Yombe Dabai wanda Alh. Sank Abdullahi ya wakilta, sai kuma Mai Martaba Sarkin Gwandu Alh. Iliyasu Bashar wanda Wazirin Gwandu ya wakilta tare da Sarakunan Gwandu, Argungu, Yauri da Zuru.
" A Duniyar nan wadanda mutane suka fi mutaauntawa sune shugabannin addini, musamman Afrika da Najeriya muna rike da addini kwarai da gaske, duk abin da ya shafi addini ko malaman addini ana daukan shi da muhimmanci kwarai da gaske.Saboda haka ina kira ga malaman addini kada su yadda yan siyasa su ja hankalinsu. Su rike wannan koyarwa da Allah ya basu na zaman lafiya doin babu wani addini da ya koyar da tashin hankali.Saboda haka ina kira garessu, mu koma ga litattafan mu, mu yi koyarwa bisa abin da ke rubuce a cikin litattafan mu domin zaman lafiya da ci gaban al'umma gaba daya" - Rev Zakka Peter
Wannan taron wata kungiya mai suna King Abdallah bin Abdul-azeez for inter-religious and inter cultural dialogue wanda ke da hedikwatarta a Vienna na kasar Austria suka zabi mutane 21 a nahiyar Afrika baki daya domin samun horarwa na jakadun zaman lafiya ciki har da Rev. Zakka Peter daga Najeriya.
Taron na bana wanda ke da taken "Addini da tuntuban juna sune makamin kariya tare da kaucewa tashin hankali a cikin al'umma" karkashin babban bako Sen. Abubakar Na'amo Abdullahi, wanda Rev Zaka ya fara da yin bayanin ginshikai ga maudu'in gabatarwar taro tare da fayyace bagire na kundin bayani. Kuma daga bisani Most Rev. Edmund E.A. Kanya ya yi jawabi kan muhimmancin zaman lafiya kamar yadda yake a Injila wanda ke nuna cewa wajibi ne a zauna lafiya tsakanin al'umma.
1. Dagab cikin wadanda suka yi bayani awajen taron sun hada da Prof. Muhammed Ka'oje Abubakar, kuma tsohon Ministan Kimiyya da fasaha wanda ke wakiltar Muslim Perspective.
2. Most Rev. Edmund E.A. Kanya Arch Bishop na Kaduna kuma Bishop na Diocese na jihar Kebbi, wanda ke wakiltar Christian Perspective
Hakazalika taron ya sami wakilcin halarcin jami'an tsaro, kungiyoyin sa kai da sauransu a fadin jihar Kebbi wadanda suka hada da Daraktan Sharia na jihar Kebbi, wakilin Kwamishinan yansanda na jihar Kebbi, NIS, NSCDC, FRSC, kungiyoyin CAN, JNI, MSSN, WOWICAN, YOWICAN, MIYETI ALLAH, Vigilante, Boys Brigade, bugu da kari taron ya sami halarcin kallabi tsakanin rawunna Mrs. Briska Gwazawa,
Daga karshe dai, an yi na'am da cewa jihar Kebbi ce jiha da ta fi kowace jiha kwanciyar hankali a fadin Najeriya, sakamakon haka aka jaddada muhimmancin ci gaba da maimaita kasaitaccen taro irin wannan nan ba ada dadewa ba a cikin jihar Kebbi.
DAGA ISYAKU.COM
Shiga shafin mu na Facebook facebook.com/isyakuweb
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0
Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
WAYAR KA TA LALACE KO KANA BUKATAR FLASHING?
Garzaya zuwa SENIORA TECH,shago mai lamba 50, hawa na sama gefen hagu,TAUSHI PLAZA , yamma daga gidan marigayi Waziri Umaru,kan Tiltin Ahmadu Bello, Nassarawa, Birnin kebbi jihar Kebbi. Barka da zuwa gidan sauki wajen gyaran wayar salula a garin Birnin kebbi.

Post a Comment