A shekaran jiya ne shugaban kwamitin harkokin man fetur na majilisar dattawa, Sanata Kabiru Marafa wanda yake wakillatar Zamfara ta tsakiya a karkashin jam’iyyar APC, ya bayyana dalilai guda goma wadanda zai sa jam’iyyar APC ta gaggauta tsige gwamnar jihar Zamfara Abdulaziz Yari. Marafa yana daya daga cikin na gaba-gaba wajen neman tsayawa takarar gwamnar jihar Zamfara, ya yi wannan bayani ne a Abuja ranar Lahadi, inda ya bayyana cewa, kwamitin zartarwa wanda Kwamared Adam Oshiomhole yake jajoranta da su tsaida duk wandanda gwamnan yake ikirarin cewa su suka lashe zabubbukan fidda gwani na jam’iyyar. Marafa yana daya daga cikin wadanda suke goyon bayan shugaba Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa, dole su tsayar da makircin da gwamna da kuma magoya bayansa suka wa jam’iyyar APC da kuma hamayya da takarar shugaban kasa karo na biyu.

“Ya kamata a tsige gwamnar bisa rashin da’a da kuma karya dokar jam’iyyar da yake yi. Ya zama wajibi a dauki tsauraran matakai wajen kare dokokin jam’iyya domin a cimma burin jam’iyya, inji shi.

A cewar Marafa, dalilan guda goma su ne; kokarin karya dokar kwamitin na gudanar da zaben fidda gwani ta jihar Zamfara.
Gwamna Yari ya jajoranci jami’an da ke gudanar da zabe da su soke zaban da aka gudanar ba tare da sanin hukumomi ba.

“Ya taimaka wajen kawo rikici wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutum shida, tare da raunata mutane masu yawa wadanda suka hada da mata da kuma kananan yara a ranar 3 ga watan Oktoba ta shekarar 2018.

“Ya sabawa umurnin shugaban jam’iyya kwamared Adams Oshiomhole wanda ya janyo asarar rayuka.

“Ya sanar da sakamakon zaben da baya kan ka’ida, wanda yin hakan ya sabawa umurnin kotu.

“Ya hana jam’iyyar APC tsaida dan takara sakamakon sanar da zaben da baya bisa ka’ida ba ranar bakwai ga watan Oktoba ta shekarar 2018.

“Ya janyo rarrabowan kai da kuma rashin kauna ga ‘ya’yan jam’iyyar APC a jihar Zamfara.
“Ya yi hayan kungiyoyi masu zaman kansu wajen gudanar da bayani a kan lamarin kafin yanke hukuncin kotu.

“Ya yi watsa da duk wata dauyi da ta rataya a kansa na shugabanci, inda ya janyo kashe-kashe, fyade da kuma yin garkuwa da mutane wanda ya kamata ya kare su, wannan ya janyo wa jam’iyya APC bakin jini a nan cikin gida da kuma wajen wannan kasa.

“Ya kashe kudadan shiga na jihar Zamfara wajen daukar nauyin masu kin yarda da duk wata doka da shugaban wannan babban jam’iyyar tamu wato Kwamared Adams Oshiomhole ya kawo” inji Sanata Kabiru Marafa.

Sources: leadershipayau.com

Post a Comment

 
Top