Mai taimaka wa shuga Buhari ta fannin kafofin sada zumunta Femi Adesina, ya ce shugaba Buhari ya ce duk wanda ke jin cewa yana da wata kasa da ta fi Najeriya zai iya tafiyarsa. Adesina ya ce Buhari ya yi wadannan kalaman ne a lokacin da ya karbi bakoncin wanda zai yi takara na jam'iyyar APC a jihar Kwara a 2019.

Hakazalika Adesina ya ambata wajen da shugaba Buhari ya ce "wadanda kuma suke jin basu da wata kasa da ta fi Najeriya, za su tsaya kuma su ceci Najeria".

"Ba sai ka sa kaki ne zai nuna kishin kasa ba, abin da na fada a 1984 yana da tasiri har yau, bamu da wata kasa da ta fi Najeriya. Wadanda suke jin cewa suna da wata kasa bancin Najeriya, ai za su iya ficewa . Mu za mu tsaya a nan mu ceci Najeriya".

Shugaba Buhari ya bukaci yan Najeriya su kasance masu kaunar kasarsu Najeriya.

Shiga shafin mu na Facebook facebook.com/isyakuweb Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0 Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

KANA ZAUNE A BIRNIN KEBBI? WAYAR KA TA LALACE KO KANA BUKATAR FLASHING? 

Garzaya zuwa SENIORA TECH,shago mai lamba 50, hawa na sama gefen hagu,TAUSHI PLAZA , yamma daga gidan marigayi Waziri Umaru,kan Tiltin Ahmadu Bello, Nassarawa, Birnin kebbi. Barka da zuwa gidan sauki wajen gyaran wayar salula a garin Birnin kebbi.

Post a Comment

 
Top