" Wallahi Tallahi na rantse da Allah Ubangijina matukar Matasan Gonin Gora za su cigaba da kawo mana tashin tashina a jiharmu ta Kaduna, to zan rushe wannan gari gaba daya in mayar da shi Fili, domin ba zamu zuba ido wasu tsiraru na haifar mana da matsala suna jefa Jama'a cikin halin tsoro ba, babu wanda ya fi karfin gwamnati".

Kalaman Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmad El Rufa'i kenan, lokacin da yake amsa tambayoyin jama'ar jihar Kaduna a cikin shirin Hannu da yawa na gidan Rediyon tarayya na Kaduna da ake gabatarwa yanzu haka kai tsaye akan halin da tsaro ya ke ciki a jihar Kaduna tun bayan sanya dokar hana walwala a fadin Jihar.

Gwamnan El Rufa'i ya tabbatar da cewar baya cikin Kaduna a ranar da hargitsi ya tashi yana Abuja, kuma cikin gaggawa ya yanke abinda yake ya nufo Kaduna, akan hanya ne ya ga cunkoson motoci ya tambaya aka ce mishi matasa ne suka tare hanyar Gonin Gora, haka ya fito ya nufi wurin Matasan na ganin shi suka gudu, akabi aka kamo su suna hannu a halin yanzu, saboda haka ya bukaci dattawan yankin su dauki matakin dakile Matasan yankin aikata haka, idan kuma ba su hanu ba wallahi za su gamu da fushin gwamnati.

Post a Comment

 
Top