Za mu gurfanar da shi a kotu – Gwamnatin Kano
Mawallafin jaridar Daily Nigerian da ke fitowa a Intanet, Jaafar Jaafar ya ce ya saki bidiyon da ke zargin Gwamnan Jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje yana karbar cin hanci da rashawa da aka yi zargin sun kai Dala miliyan 5 (kimanin Naira miliyan 1,800) ne don ganin an magance cin hanci da rashawa da ake fama shi a kasar nan.
Jaafar Jaafar ya bayyana haka ne lokacin da yake tattaunawa da Aminiya a shekaranjiya Laraba, inda ya musanta zargin cewa siyasa ce ta sa ya saki hotunan bidiyon, ya ce a daidai wannan lokaci ne hotunan bidyon suka zo hannunsa.

Har ga Allah ba siyasa ce ta sa na saki hoton (bidiyon) ba, na sake su ne don a yi maganin cin hanci da rashawa. Magana ake yi ta yaki da cin hanci, to kuma ga shi mun samu hujja a hannu kuma don muna tsoron kada a zarge mu sai mu ki saki kowa ya gani. Ashe ma ba aikin jaridar muke yi ba ke nan? Da a ce manufar siyasa ce ta sanya muka saki hoton (bidiyon) nan, to da sai an kusa zabe za mu fito da shi. Ko kuma da hakan ne a ranmu to da a lokacin da za a yi zaben fid da gwamni za mu saki don a wannan lokaci muna da tabbacin jam’iyya za ta iya hana shi takara,” inji shi.

Jaafar Jaafar ya kara da cewa a wasu jihohin ’yan laifuffuka ne aka samu ’yan takara da su amma aka hana su yin takara gaba daya.

Mawallafin jaridar Daily Nigerian din ya kara da cewa; “Mun dade da sanin cewa Gwamnan yana tafka wannan aika-aika ta karbar na-goro a wurin ’yan kwangila. Kuma su ’yan kwangilar ne da kansu suke yin korafi a kan halin Gwaman. Hakan ya sa aka shawarce su da su dauko hotonsa yana karbar na-goron domin a samu hujjar da za ta tabbatar da abin da suke fadi, domin sai kana da hujja kake kama barawo idan ba ka da ita shi zai iya kama ka. Na yi ta bin mai hoton ya ba ni, amma ya rika nuna tsoro a harkar. Da kyar ya yarda ya ba ni su a wannan lokaci.”

Jaafar ya musanta batun cewa ya fitar da iyalansa zuwa kasar waje inda ya ce, “Muna nan a cikin kasar naan sai dai mun bata a rububi. Kin san abin ya jawo ana barazana ga rayuwata. Ba zai yiwu mutum ya fito ya bayyana inda yake ba, kasancewar jami’an gwamnati ko wadansu magoya bayan Gwamnan za su iya kai wa mutum farmaki, dole mutum ya nemi hanyar tsira da rayuwarsa.”

Tun lokacin da jaridar Daily Nigerian ta fitar da labarin zargin Gwamna Ganduje kan karbar cin hanci da rashawa daga wadansu ’yan kwangila lamarin yake ta daukar hankalin al’ummar Jihar Kano da kasa baki daya.
Jaridar ta Daily Nigerian ta fitar da hotunan bidiyo uku inda aka nuna Gwamna Ganduje yana karbar na-goro daga hannun wani dan kwnagila, hotunan bidiyon da suka watsu a kafafen sada zumunta na Intanet.

A nata bangare Gwamnatin Jihar Kano ta fitar da wata sanarwa dauke da sa hannun Kwamishinan Watsa labarai na Jihar Kwamared Muhammad Garba inda ta musanta zargin da kuma sahihancin bidiyon inda ta ce hadin hoto ne kawai.
Gwamnatin ta ce za ta gurfanar da jaridar Daily Nigerian da mawallafinta Jaafar Jaafar a gaban kotu. Kuma gwamnatin ta zargi ’yan adawa musamman bangaren Kwankwasiyya da ke rikici da kitsa lamarin. Sanarwar ta ce ’yan adawa ne “suka shirya wannan abu don a rage farin jini da daukakar Gwamnan da kuma rage yawan kuri’ar da ake sa rai Jam’iyyar APC za ta samu a zaben 2019,” inji sanarwar.

Kafin nan gwamnatin ta zargi Jaafar Jaafar cewa yana kokarin bata sunan Gwamnan ne bisa dalilin rashin samun biyan wata bukatarsa daga gwamnati. “Dama wannan dan jarida sananne ne a kan bata sunan mutane. Gwamnatin Jihar Kano tana kira ga al’ummar jihar su yi watsi da duk wani abu makamancin haka, kasancewar Gwamnan yana ci gaba da gudanar da ayyukan raya kasa don ci gaban al’ummar jihar,” inji shi.
A wata hirar da Gidan Rediyon BBC, Jaafar Jaafar ya ce babu batun kage ko sharri a cikin labarin nasa. Ya ce jaridarsu ba ta yin kage tana buga sahihan labarai ne. Kuma kafin ta buga labari sai ta tace ta tabbatar da sahihancinsa. “Don haka wannan labari gaskiya ne, muna da hoton bidiyo a kan hakan fiye da 15, sannan kafin mu saki labarin sai da muka nemi kwararu a kan na’urar kwamfuta suka tabbatar mana cewa hoton ba wani abu ne da kake yin siddabaru ba, hotuna ne na gaskiya,” inji shi.

Ya ce a shirye yake ya gurfana a gaban kotu “Wanda yake tsoron zuwa kotu ba ya da gaskiya ne. Ga abu a zahiri an nuna ana karbar kudade daga ’yan kwangila. Kudade ne da yawa ake karba daga wuirn ’yan kwangila daban-daban,” inji Jaafar Jaafar.
Ya ce ba wanda ya hada baki da shi don cimma wata manufa ta siyasa “Ba a hada baki da ni, ko shi Kwankwason idan maganar gaskiya ta bayyana a kansa ina yin labari a kai. A kwanan nan ma sai da na yi labari a kan bai wa surukinsa takarar Gwamna da ya yi. Kuma har yanzu ina kan bakata cewa abin da Kwankwason ya yi bai dace ba.”
Majalisar Dokokin Jihar Kano ma ta shiga cikin lamarin ta hanyar kafa kwamiti mai wakilai bakwai don ya binciki gaskiyar hoton bidiyon.

Kafa kwamitin da majalisar ta yi ya biyo bayan gabatar da kudurin gaggawa da Mai tsawatarwa a majalisarAlhaji Labaran Abdu Madari daga Karamar Hukumar Warawa ya yi.
Shugaban Majalisar Alhaji Kabiru Alhassan Rurum ya ba kwamitin wa’adin wata guda ya gabatar da rahotonsa gaban majalisar. ’Yan kwamitin sun hada da Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar, Alhaji Baffa Babba Dan’agundi a matsayin shugaban, sai Labaran Madari da Zubairu Massu da Garba Ya’u Gwarmai da Abdul’aziz Garba Gafasa da Abubakar Uba Galadima da Mujitaba Aminu wanda zai zama sakataren kwamitin.

Da yake yi wa manema labarai jawabi kan nauyin da aka dora musu, Alhaji Baffa Babba Dan’agundi ya ce “Za mu binciki hakikanin gaskiyar wadanan hotunan bidiyo da wurin da suka fito za kuma mu binciki ainihin wanda ya bayar da cin hancin, idan abin ya tabbata, kuma za mu gabatar da rahotonmu ga majalisa ita kuma za ta zartar da hukuncin da ya dace. Idan kuma abin ba gaskiya ba ne za mu umarci gwamnatin Jihar Kano ta gurfanar da jaridar da mawallafinta gaban kotu.”
Dan’agundi ya ce sun dakatar da gwamnatin kan batun gurfanar da dan jaridar a gaban kotu har zuwa lokacin da kwamitinsu zai gabatar da rahotonsa, don guje wa bata al’amuran gaba daya.

Ya ce, “Za mu yi aiki da gaske wajen sauke nauyin da aka dora mana za kuma mu yi duk abin da ya kamata wajen fito da sakamako na gaskiya.”
Sai dai lokacin da aka nemi sanin ko kwamitin yana da damar tsige Gwamnan idan har aka same shi da laifi, sai aka shaida wa Aminiya cewa “ya yi wuri a yi wannan maganar a yanzu.”

Mai magana da yawun Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, Hajiya Binta Spikin ta musanta sa hannun jagoransu a batun bayyanar hoton bidiyon zargin Gwamna Ganduje da karbar rashawa inda ta ce “Kowa ya san ba mu da gwamnati ba mu da wani mukamin siyasa. Idan an duba ba wanda ya ga wani da ke da alaka da Kwankwasiyya a cikin wannan hoto ballantana a zarge mu. Duk mutumin da yake tunanin da sa hannunmu a cikin wannan lamari, ya fadi son ransa ne kawai.”

Hajiya Binta ta yi fatan majalisa za ta gudanr da aikinta yadda ya kamata wajen tabbatar da hukunci a kan Gwamna Ganduje. “Kasancewar ga hujjoji nan baro-baro muna fatan doka za ta yi aikinta a kansa.’Yan majalisa su yi gaskiya wajen fitar da sakamakon bincikensu wannan shi ne fatanmu,” inji ta.


Sakataren Tsare-Tsare na Jam’iyyar PDP reshen Jihar Kano Alhaji Sanusi Surajo Kwankwaso ya bayyana cewa sharrin da Gwamna Ganduje yake bin Kwankwaso da shi ne Allah Ya mayar masa kansa. “Akwai lokacin da Ganduje yake cewa zai fede biri har wutsiyarsa, to sai ga shi nan an fede nasa birin. Na tabbata da a ce Kwankwaso yana da abin fadi ko abin kunya makamancin wannan, to da tuni mutanen Ganduje ya fito da shi don duniya ta sani,” inji shi.

Post a Comment

 
Top