Sashen Jakar Magori na Mujallar isyaku.com ya samo mman labarin wani barawo da ya fada hannu bayan an cafke shi sakamakon satar wani talabijin Plasma a cikin dakin barci na basaraken kasar Assin Brofoyedu, Nana Kwaku Agyepong II a kasar Ghana ,bayan basaraken ya je ziyarar aiki a wani gari.

Bayan basaraken ya dawo, sai ya lura cewa barawo ya sace masa wasu kudadensa tare da talabijin Plasma a bangon dakin barci da ke gidansa. Sakamakon haka aka hada samari aka shaida masu abin da ya faru. Bayan dan lokaci, sai ga barawon an kamo shi kuma aka gano talabijin din da ya sace a dakin wani abokinsa da ke wata unguwa.

Saura kadan a kashe barawo sakamakon duka kafin yansanda su iso wajen amma basaraken ya hana a kashe barawon.

DAGA ISYAKU.COM

Copyright, do not copy and paste our news on your blog without expressed permission from us. 

Shiga shafin mu na Facebook facebook.com/isyakuweb

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0

Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

WAYAR KA TA LALACE KO KANA BUKATAR FLASHING? 

Garzaya zuwa SENIORA TECH,shago mai lamba 50, hawa na sama gefen hagu,TAUSHI PLAZA , yamma daga gidan marigayi Waziri Umaru,kan Tiltin Ahmadu Bello, Nassarawa, Birnin kebbi jihar Kebbi. Barka da zuwa gidan sauki wajen gyaran wayar salula a garin Birnin kebbi.

Post a Comment

 
Top