Mai ba wa gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje kan harkokin siyasa, AMBASADA RASHIDA ADAMU ABDULLAHI MAISA’A, ta yi fice da zarra a fagen shirya finafinai da kuma farfajiyar siyasa a jihar Kano. A matsayinta na kwararriya kan shirya finafinan bidiyo ta samu zantawa da Editan LEADERSHIP A YAU LAHADI, NASIR S. GWANGWAZO, musamman kan badakalar hoton bidiyon da ya bayyana, inda wani dan jarida mai jaridar yanar gizo, Malam Ja’afar Ja’afar, ya yi zargin cewa gwamnan jihar ta Kano ya na amsar cin hanci ne a ciki. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

Me za ki ce game da bidiyon da a ka saki kwanan nan a na zargin gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, da amsar cin hanci?

To, wannan bidiyo da Ja’afar Ja’afar ya saki ai duk dan jaridar kirki ya san cewa ba zai yiwa wani mutum tarko ba, don ya tona ma sa asiri. Zuwa za ka yi ka yi hira da dan jarida ma, amma idan daga baya ka ga hirar ba ta yi ma ka ba, ka na iya zuwa ka canja ta ko ka janye ta, ballantana kuma a ce mutum ya kafa wani tarko har ya dauki wani da bidiyo ya je ya watsa da sunan tona asirinsa. Idan ba ka da wata bukata a karkashin kasa kan wannan mutum da ka ke son tona wa asiri ba, ba yadda za a yi ka yi wannan abin. Kuma misali kamar bidiyon da ya ce akwai bidiyo, ai ni ’yar wasan kwaikwayo ce; na san yadda a ke tace hoto (editing). Na fada cewa, zan saki bidiyo kamar yadda a ka nuna mai girma gwamna ya na mika kudi ba tare da a na ganin mutumin da ya miko kudin ba kuma tsawon shekarun da a ka yi a na amsar kudin kayan mai mika kudin guda daya ne, kamar aljanu ne su ke mike ma sa tunda ba a nuna ma na mutumin da ya kawo ba na wanda har za ka iya shiga ofishin gwamna ka dauke shi, to ta ina ya saka kyamarar?

Ba ki tunanin ko irin kyamar nan ce ta zamani a jikin biro a makale?
To, ai idan haka ne kyamarar ba za ta yi rawa ba kenan. Za ta rika daukar abu daya ne kawai tunda biron ya na jikinsa ne watakila a makale a gaban aljihunsa.
Idan kuma shi ne ya ke motsawa fa?

Ai komai motsi ba ta isa ta dauko hannunsa ba, idan ba daga ta ya yi ya kai ta kasa ba. Karya ya ke yi, domin mu na da ilimin wannan kan harkar kyamara, saidai mu nuna wa Ja’afar Ja’afar cewa shi dakiki ne, bai ma san me ya ke yi ba. Ni na ce a matsayina na kwararriya kan harkokin hada hoton bidiyo wacce ke da kayan aiki na zamani kuma kannena su ke yin aikin, zan nuna wa Ja’afar Ja’afar yadda a ke hada hoton; zan dauki wannan kujerar da ya ce ya dauki gwamna a kai da kayan da ya ke a jikin gwamna, ku saurare ni zan saka Ja’afar ne kamar ya na karbar wannan kudin, don duniya ta gane cewa raina mu su hankali ya ke yi.

A matsayin me za ki saka?

A matsayin na shi bai san aikin ba kuma a matsayin a san cewa sharri ya ke kirkira, domin ba a kan gwamnan Kano ya fara yi ba. Idan za ka tuna a shekarar 2017 ai ya yiwa Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II. Wane irin sharri ne bai buga ba a wannan jaridar ba?

Wane irin sharri ya yi ma sa?

Ya yi ma sa sharri cewa ya saci kudade ya je ya gyara gida. Gidan nan da Sarkin nan ya gyara fa, idan ya mutu ba za a binne shi da shi ba. To mene ne laifi a ciki? Amma da ya ke Ja’afar masharranci ne, wanda abinda ma zan kira shi da shi daga yanzu shi ne Khadimul Sharri, ba irin kalubalen da bai rika yiwa Sarki ba. Amma da ya ke akwai Allah, a cikin lokaci kankani mutane su ka gane cikin sati, magana ta wuce. To, yadda wannan maganar da Mai Martaba Sarki ta wuce, haka ita ma maganar Mai Girma gwamna za ta wuce, don tuni ma an juya bidiyon ta yadda gwamnan ne kuma ya ke mika kudin, don a nusar da mutane yadda a ke iya yin siddabarun hoto a wannan zamani cikin sauki kuma wasu masoyansa ne su ka yi, ba wani daga cikin gwamnati ba. To, ni kuma zan yi wanda fuskar Ja’afar ce ta ke karbar kudin.

To, ba ki jin cewa idan ki ka yi wannan shi Ja’afar zai iya kai ki kara?

Idan Ja’afar zai kai ni kara, shi fa Mai girma gwamna a ke magana fa. Shi kuma me za a yi ma sa? Zan yi wannan bidiyon ne don a gane yadda gaskiyar abin ya ke. Har ma zan dauki wanda ni na ke mika wa Ja’afar bidiyon a hannunsa, wanda shi a nasa an samu bambancin rashin gogewa, domin hannu kawai a ke gani ya na mikowa, wanda riga daya ce duk tsawon shekarun da a ka yi a na mika kudin. Mutumin da zai dauki cin hancin Daloli ya bayar, amma ya zauna shekara guda da riga daya a jikinsa, ai wannan abin dubawa ne! Kamar wasan dokin yara!

Akwai tambayar da wani ya ke yi cewa, shin me ya sa da a ka ba wa gwamna kudi a cikin ofishinsa ya ke kokarin boye su a cikin aljihu?

To, wannan ma abu ne da ke nuna rashin sahihancin bidiyon, domin a matsayinsa na gwamna d a ka kai ma sa kudi a gidansa ko a cikin ofishinsa, amma a ce ba shi da wata ma’ajiya ta zuba kudi (safe)? To, tsoro ya ke yi ya shiga gida da kudin a kwace ko kuma jami’an tsaronsa ya ke tsoron kada su daka ma sa wawa? Ai ba za ta taba yiwuwa ba. Kuma abinda na ke so mutanen jihar Kano su gane shi ne, a matsayinsu na ’yan kasuwa, shin ba zai yiwu a ce a kawo wa mutum kudin kasuwancinsa gida ko ofis ba, idan ma ta kasance bidiyon na gaske ne? Ai ni zan iya cewa mutum ya zo mu yi hoto ko don a ga shaidar ka kawo kudin kasuwancin da mu ka yi.

Amma ba ki tunanin nan gaba wasu bidiyon za su fito wadanda su ke bada amsa kan wadannan amsoshi naki tunda ya ce bidiyon sun kai 15?

To, bari ka ji na gaya ma ka; yanzu ta kacame mu su ne saboda an fara gane makiricinsu. Mu na da labarin cewa su na can a Lagos su na fadi tashin yadda za su dora muryar Dr. Abdullahi Umar Ganduje ko su gyara bidiyon ya yi kyau. To, kuma Allah ba zai ba su nasara ba! Bari na ba ka misali da abokin aikina Sadi Sidi Sharifai, ai ya na yin muryar Ibro, wacce ba ka isa ka ce ba tasa ba ce, sannan ya na yin muryar mace. Sadi Sidi akwai muryoyi da ya ke yi namu na jarumai mata, ballantana kwamfuta. Saboda haka mu a matsayinmu na ’yan fim mu na masu ba wa Ja’afar shawara idan zai yi wani abu na editing ya rika taka-tsantsan ya na neman shawara. Me ya sa manyan jaridu irinsu LEADERSHIP da sauransu ba sa buga irin wannan sharrin? Ko ku ba ’yan jarida ba ne? Ai akwai wani minista da wani gwamna da su ka yi batsa da mace, wanda ni na gan su da idona, amma da a ka kawo a ka ce a buga sai su ka ba za su buga ba. Amma shi wannan da ya ke dakiki ne lamba daya, sai ya ke rawar jikin bugawa. Amma ya sani Mai girma gwamna ya na da ikon kai shi gaban kotu!

Ko ki na ganin akwai sa hannun wasu ’yan siyasa a wannan badakala?

Ina yi ma ka yakinin cewa da sa hannun ’yan siyasa a wannan abin. Shi Ja’afar ai karen farauta ne.
 Mai gidansa ya na saka shi ya yi aiki.
Waye mai gidansa?

Madugun Kwankwasiyya.

Rabiu Musa Kwankwaso?

Yauwa! Kowa ya san mai gidansa ne. Kowa da irin tunaninsa; ni yanzu Dr. Abdullahi Umar Ganduje mai gidana ne, amma idan ya zo ya ce na yi abinda bai dace ba, zan nuna ma sa cewa ba haka yakamata ba. To, amma idan ka yi tuntube da mutum dakiki zai iya yi.
Amma fa an ce har kudi a ka ba wa Ja’afar kan ya rufa wannan asirin, amma ya ce ba zai karba ba.
Waye ya ba shi kudin? A matsayinsa na wanda ya iya daukar bidiyo, da a ka ce za a ba shi kudin, ai sai ya sake dauka ya tona maganar kudin ita ma ya sake ta. Mu na jira! Karya ya ke yi, makaryaci ne, bai san aikin jarida ba, ya kamata ya gyara! A matsayinsa na Musulmin kirki ai koda gaskiya ne, kamata ya yi rufa wa wanda ya yi ba daidai ba asiri, amma ya kira shi ya ja kunnensa, don ya kiyaye ya daina gaba. Don haka Ina kira ga al’ummar jihar Kano da Najeriya gabadaya da su cigaba da yiwa Mai girma Dr Abdullaji Umar Ganduje addu’a ya dora kan ayyukan da ya ke yi mu su.

Amma wane hali gwamnan ya ke ciki a halin yanzu?

A lokacin da abin ya faru ni kasa barci na yi, saboda na san harkata ce ta fim a ka kulla wa wannan bawan Allah sharri a kanta, har zuwa na yi na shiga tsarin wayar sadarwa na kashe kudina a ke tura wa mutane a layikansu, don a wayar da su, amma abinda ya ba ni mamaki shi ne, shi gwamnan ko a jikinsa; a washegari ma ya je bikin bude ayyuka a karamar hukumar Fagge da duba wasu manyan ayyuka na gadoji da gwamnatinsa ke gudanarwa, kuma washegari da safe ya tafi gaishe-gaishen mutuwa. Yanzu haka ya tafi wajen Shugaba Muhammadu Buhari don ya halarci wata ganawa a tsakaninsu irinta masoya, don cigaba da ayyukan da su ke yi na alheri. Hatta wannan hirar da na ke yi, wallahi bai san zan yi ta ba. Amma shi Ja’afar hankalinsa ya ki kwanciya har cewa ya ke yi wai a na yi ma sa barazana da rayuwarsa. To, ai da ma wanda duk ya ke kulla sharri, haka siddan zai ji hankalinsa ya ki kwanciya. Shi kuwa mai girma gwamna tunda ya san bai yi ba, babu abinda ya dame shi, shi ya sa ya ke fita ko’ina gari, mutanen gari su na cigaba da kai ma sa caffa! Kai, bari na takaice ma ka bayani ma; a jiya sai da su ka yi walima!

Ta meye?

Mai girma Mataimakin Gwamna, Dr. Nasiru Yusuf Gawuna, a ka karrama a makarantar da ya yi, jami’ar Danfodio ta Sokoto, inda daliban da su ka yi karatu da shi su ka zo su ka karrama shi, kuma mai girma ya halarta. Ba ya cikin damuwa, mu ne dai da mu ke tare da shi mu ke ta wannan babatu, saboda bai kamata a yi zalunci mu yi shiru ba a matsayinmu na wadanda mu ka san harkar fim! Don haka Ina godiya ga ’yan fim bisa irin hadin kan da su ke ba mu da gudunmawar da su ke ba wa wannan gwamnati.

Post a Comment

 
Top