Me ya sa kowa ya ke cewa a binciki Jaafar Jaafar amma babu me cewa a binciki Ganduje?

Me ya hana Buhari daukar mataki a jihar da ya fi masoya? 

Me ya hana EFCC shiga lamarin? 

'Yan Majalisar dokokin jihar Kano makiya Buhari ne,  yaudarar Kanawa suke yi ba wani bincike da za su yi. 

Duk karyar da za a yi a gidan Rediyo da jaridu ba zai canja komai ba. 

Wannan badakala za ta shafi zaben Buhari a Kano.

Gwamnatin jihar Kano na ba wa 'ya'yan Talakawa kwaya da makamai. 

Idan ba a canja Ganduje ba ba za mu zabi APC ba. 

Idan ba gaskiya ba ne ya karbi Dalolin ya fito ya karyata. 

Duk sakarcinka ba za ka ce bidiyon nan karya ba ne. 

Idan DSS ko EFCC suka fito suka ce wannan bidiyon karya ne shikenan. 

Akwai mutane da dama 'yan Jam'iyyar APC ne an rubuta korafi a kansu amma Buhari ya kasa yi musu komai. 

Duk wanda hakkin Al'umma yake hannunsa ya ci amanar su to akwai ranar kin dillanci. 

Daga lokacin da Tutar Jam'iyya ta zama ita ce zabinka ba mutum ba ka samu matsala. 

Duk wanda ya ga ana laifi ya ja baki ya yi shiru yana cin gajiyar wannan laifin. Ko MATSORACI ne ko MUNAFUKI ne. 

'Ya'yan Talakawa ku daina yarda ana mayar da ku 'yan kwaya ana ba ku makamai saboda kare aljihun wani. Su fito da 'ya'yan su ko 'ya'yan 'yan uwan su.

Post a Comment

 
Top