DAGA MUKHTAR HALIRU TAMBUWAL SOKOTO
A ranar Litinin din da ta gabata Hukumar Zakkah da Wakafi ta Jihar Sakkwato ta karbi wakafin fili daga hannun Hajiya Fatima Muhammad.
Hajiya Fatima, ta bayar da filin nata dake Unguwar Guiwa layout a matsayin wakafi domin Allah ta da nufin gina masallaci.
Cikin jawabin da ta yi lokacin bada filin ta ce "na yi wannan ne lura da Hadisin Annabi S.A.W dake nuni da idan mutum ya mutu abu uku ne za su amfane shi, ciki har da wanda ya gina masallaci" (Sadakatul Jariya).
Ta kara da cewa "Na zauna na yi tunanin wannan Unguwar babu masallaci, kuma shiyar ta kunshi jama'a, sai na yanke shawarar naba da wannan filin domin a yi masallai, kuma ga bohol dina nan gaban gidana a jawo a yi famfuna a yi wakafi, kuma hukuma na iya sarrfa filin zuwa duk abinda zai amfanar da al'umma".
Hajiya Fatima ta gabatar da taswirar masallacin da kudi naira dubu dari takwas (800,000.) domin fara aiki da su.
Hajiya Fatima ta yi kira ga 'yan uwanta Mata da sauran al'umma da su yi hubbasar shiga cikin irin wadannan ayyuka domin taimakawa musulunci da al'ummar musulmi baki daya.
Shugaban Hukumar Malam Muhammad Lawal Maidoki, kuma mataimakin sakatare mai kula da kasashen yankin Afirika ta yamma, na kasashen Duniya masu sha'anin zakka da wakafi, (Sadaukin Sakkwato) ne ya jagoranci karbar wakafin tare da wasu ma'aikatan hukumar.
A cikin jawabinsa na karba, ya bayyana matar a matsayin mace ta farko da ta taba bada wakafin wuri domin gina wani abin amfani ga bayin Allah, kuma ta biyu a bada wakafin kudi, haka ma ya yi kira ga sauran mutane da su dubi muhimmacin yin wakafi domin Allah da samun tsira gobe Lahira.
Shugaban ya bada tabbacin za su yi kokarin kula da wurin a matsayin su wadanda sharia ta dorawa kula da shi. Sadaukin ya bada tabbacin za a yi duk abinda ya kamata na shari'a, samar da shaidu, sanya hannu da fitar da iyakar wurin dan cika sharudddan wakafi.
A karshe ta zagaya da wakilan hukumar cikin wannan wurin.
Daraktan tsare-tsare na ma'aikatar Malam Murtala Garba Alkali ne ya jagoranci yin addu'a ta musamman ga wannan baiwar Allah.
Daraktan zakka Malam Muhammad Umar Hamma Ali, ta kudi, Hajiya Huraira Isah Illo, Jami'in Hulda da 'yan jarida Malama Abubakar Sadik, na cikin wadanda suka shaidi karbar wannan wakafin tare da sauran ma'aikatan hukumar.
Ko kwanan baya hukumar ta karbi wani gida da ofishi wanda wasu bayin Allah suka bada a matsayin sadaka.
Post a Comment