An sami barkewar tarzoma a  Ilogbo-Ekiti da ke karamar hukumar Ido/Osi a jihar Ekiti bayan al'ummar garin sun kori basaraken garin tare da iyalinsa daga garin bayan jama'n garin sun zargi basaraken da daure ma ayyukan kungiyoyin asiri gindi. Majiyar isyaku.com ta ta ce masu tarzomar sun barnata motoci da kuma dukiyar jama'a ranar Talata yayin da suke gudanar da tarzomar.

Jama'an garin sun yi zargin cewa yawancinsu sun fuskanci barazana da tursasawa daga yan kungiyar asiria agarin wanda hajama'an ke zargin cewa wani 'dan basaraken mai suna Adeleye Ajayi ke jagoranta. Wata majiya ta ce an taba koran 'dan basaraken a jami'a sakamakon ayyukan kungiyoyin asiri a jihar Ondo shekara 5 da suka gabata.

Majiyar isyaku.com ta ce mutuwar wani karamin yaro a yanayi irin na kisan yan kungiyar sairi ne ya zafafa wannan tarzomar

DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafin mu na Facebook facebook.com/isyakuweb

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0

Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

WAYAR KA TA LALACE KO KANA BUKATAR FLASHING? 

Garzaya zuwa SENIORA TECH,shago mai lamba 50, hawa na sama gefen hagu,TAUSHI PLAZA , yamma daga gidan marigayi Waziri Umaru,kan Tiltin Ahmadu Bello, Nassarawa, Birnin kebbi jihar Kebbi. Barka da zuwa gidan sauki wajen gyaran wayar salula a garin Birnin kebbi.

Post a Comment

 
Top