Ubangiji Ya san zuciyata batada burin data wuce na saita Nijeriya a tafarkin da zakuji dadi nan gaba.
Akwai tsananin wahala yayin da kake qoqarin kawo canji a kasa, muna iya qoqarinmu koda abokan hamayyar mu sun sani muna qoqarim ganin mun daura kasarnan a turban data dace. Munyi laifi ga wadannan yan siyasa masu akwatunan kudi, mun san bazasu ta6a yafe mana ba.
Laifin shine, mun toshe musu duk wassu hanyoyin dasuke bi wajen sace dukiyar al'ummah, ba damuwar su bane koda kasarnan zata kama da wuta, Idanma ta Kaman, zasu iya sayarda tokan su fice kasashen qetare.
Sun shirya tsaf da qarfinsu domin wargaza shirin da muka soma na saita wannan kasar tamu.
Basuda damuwa koda da qwayan zara gameda damuwar mitanen kasar nan
Bamuda za6i, za6in nakune mitanen Nijeriya, idan kun amince da qoqarinmu, zaku iya za6anmu a karo na biyu domin cigaba daga inda muka tsaya.
Hakan zai amfanemu Baki daya, idan kuma baku aminta damu ba, zaku iya komawa garesu (masu jakar kudin) domin wargaza muku rayuwar ku nan gaba (dama kasar Baki daya).
Ammana tabbas zaku tuna cewa na fada muku gaskiya, kuma na daura ku a kan turban gaskiya, kuma na mulkeku da gaskiya
Za6i naku ne domin kasar.
Na rantse tsakanina da Ubangiji ba akan siyasa nake wannan zance ba, sai don halin da kasarmu zata kasance nan gaba.
Shugaban kasa
Muhammadu Buhari.
Ya Allah ga BawanKa Muhammad Buhari yanada manufofi masu kyau ga kasarnan da mitanen kasar nan da kasar Baki daya, Ka tallafa masa, Ka bashi wazirai na gari Ka kara masa lafiya da qwarin guiwa da nisan kwana masu albarka Ya Arhamar Rahimina Ya Rabbal alamin.
Madogara Bappah Abubakar
Post a Comment