isyaku.com 30-10-2018

An bayyana canjin sheka da aka ce wasu mutane mabiya akidar Kwankwasiyya  sun yi zuwa jam'iyar APC a jihar Kebbi a matsayin wani wasan yara da kuma shirin dodoriyo domin amfani da wannan dama kawai don a karbi na goro daga hannun wadanda ake so a karba ,alhalin gaba daya tsarin yaudara ce da jaddada karya.

A zantawaru da Sakataren akidar Kwankwasiyya na jihar Kebbi, Malam Mansur Sarki, ya ce " Wannan taro da aka ce wasu sun canja sheka daga akidar Kwankwasiyya suka koma APC yaudara ce kawai da kwadayi. Wasu kananan mutane ne kawai suka tara 'yan yara aka je domin a cika wa Gwamnatin jihar Kebbi fuska domin a sami wata biyan bukata.

Mutum nawa ne 'yan Kwankwasiyya na ainihi, Kwankwasiyya Amana?, babu wani dan Kwankwasiyya na ainihi, na gaske bisa akidar tafiyar da ya juya wa Engineer Rabiu Musa Kwankwaso baya. Duk wannan taron yaudara ce kawai daga wasu kananan mutane kalilan.

Hakazalika, ana zargin cewa an gan wasu daga cikin wadanda suka ce sun bar Kwankwasiyya suka koma APC suna fitar da jajayen huluna daga booth na motocinsu suna raba wa samari a gefeb filin Masallacin Idi da ke unguwar Gesse a garin Birnin kebbi da safiyar ranar Talata kafin su je fagen taron.

Wani mai fashin bakin siyasa Mal. kabiru Sani, ya yi tsokaci akan lamarin inda ya ce " Idan wasu yan Kwankwasiyya sun canja sheka suka dawo APC a gani an duk wannan ba burgewa bane, hujja na a nan shine, ai kafin wannan lokaci akwai 'yan PDP da suka koma APC a bara dubu dubatansu, ciki har da su Bello Doya daga kasar Zuru, tsohon Minista Sambawa har da tsohon Gwamna Saidu Dakingari da dimbin magoya bayanssu. Amma don Allah miye ka gan an yi masu a cikin jam'iyyar APC a jihar Kebbi kawo yanzu ?. Saboda haka kukan kurciya adai jawabi ne.

Idan kuma ka duba su kansu 'yan jam'iyyar APC yan asali a jihar Kebbi, don Allah mutum nawa ka gan wannan Gwamnati tana damawa da su a kan cewa su ne suka yi zufa wajen kwadagon ganin an dora Gwamnatin kan kujerar mulki, amma a yau sai dai su gan kurar motar wadannan shuganaiini kawai ta wuce su? gaskiya akwai gyara, su kuma 'yan Kwankwasiyya da aka ce sun shiga gidan APC a yadda take a yanzu, bismillah, ga fili ga mai doki".

DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafin mu na Facebook facebook.com/isyakuweb

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0

Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

WAYAR KA TA LALACE KO KANA BUKATAR FLASHING? 

Garzaya zuwa SENIORA TECH,shago mai lamba 50, hawa na sama gefen hagu,TAUSHI PLAZA , yamma daga gidan marigayi Waziri Umaru,kan Tiltin Ahmadu Bello, Nassarawa, Birnin kebbi jihar Kebbi. Barka da zuwa gidan sauki wajen gyaran wayar salula a garin Birnin kebbi.

Post a Comment

 
Top