Daga Isyaku Garba- Birnin kebbi - 10-10-2018 -

Jihar Kebbi ta sami kanta cikin rudanin siyasa, amma cikin lumana sakamakon gudanar da zaben fitar da gwani na mukaman siyasa da aka yi na jam'iyyun siyasa wanda manyan jam'iyyun APC da PDP suka gudanar. Saidai an kwashi yan kallo a bangaren jam'iyyar APC a jihar Kebbi sakamakon yadda wasu yan siyasa karkashin jam'iyyar APC a jihar suka rasa damar sake komawa kan kujeri da suke wakiltar jama'arsu sakamakon kaye da suka sha a hannun abokan takara a zaben fitar da gwani da aka gudanar wanda jama'a ke zargin an gudanar da shi a yanayi na rashin gaskiya, adalci balle nuna tsoron Allah duk da yake an gudanar da zabe a filin wasa na Haliru Abudu da ke garin Birnin kebbi.

A lokacin wannan zaben na yan majalisar wakilai, dan takara Muhammed Bello Yakubu ne ya lashe zaben, a wani yanayi da magoya bayan Abdullahi Muslim suke ganin cewa mahukunta sun aikata abin da suka gan dama a wajen gudanar da wannan zabe. Bisa wannan dalili, dubban magoya bayan Abdullahi Muslim suka nuna rashin gansuwa da kuma rashin jin dadin yadda sakamakon zaben ya kasance. Yanzu haka, wasu daga cikin magoya bayan Abdullahi Muslim sun rantse su fa sai sun rama rashin adalci da aka yi wa uban gidansu, duk da yake Muslim ya fitar da sanarwa yana rokon magoya bayansa su yi wa Allah su yi hakuri.

A gefe daya kuma, wanda ya lashe zaben, zagayawa ya yi ta yi yana abin da Turawa ke kira Rally, yanayi da ya dada harzuka sauran magoya bayan yan takara da suka kara tare da Bello Rilisco. Wani labari da aka tsegunta wa isyaku.com ya nuna yiwuwar sauran yan takara da suka tsaya da Bello Rilisco na shirin saka ma kura da aniyarta ta hanyar dunkule karfinsu waje daya su rama abin da wasu magoya bayansu suka kira "danniya da rashin adalci da aka nunaa mana" kamar yadda wani magoyi bayan wani dan takara ya shaida mana.

Hakazalika, A Kebbi ta Arewa, akwai babban matsala da har yanzu ke ta fadada sakamakon yadda wasu ke ganin babban kuskure ne da Gwamnatin jihar Kebbi tare da jama'iyyar APC mai mulkin jihar Kebbi suka aikata wa jama'ar wannan yankin sakamakon yadda lamurra suka kasance dangane da takara da Chiroman Kebbin Argungu Alh. Muhammed Ibrahim Mera ya so ya yi na mukamin kujerar Gwamnan jihar Kebbi. Masu lura da al'ammurra sun yi harsashen cewa abin da ya gudana tsakanin Mera da jam'iyyar APC zai iya sa jam'iyyar ta yi mumunar asarar magoya baya a fadin jihar Kebbi, musamman a Masarautar Argungu.

Har ila yau dai a Masarautar ta Argungu, dimbin magoya bayan Alh. Hussaini Kangiwa sun sha alwashin ba Gwamnati da jam'iyyar APC mamaki a zabukan 2019. Wani magoyi bayan Alh. Hussaini Kangiwa da baya son mu ambaci sunansa ya ce " duk da yake ba da yawun maigida nake wannan magana ba, amma wallahi ina tabbata maka cewa dubu dubatan mu za mu fice daga jam'iyyar APC sakamakon rashin Dattaku, cin amana da wulakanci da aka yi mana tare da maigidanmu. Ka san APC ba addini bace, saboda haka zamu fice daga wannan gida na mugayen mutane da basu san mutuncin jama'a ba. Wallahi duk wanda ya wahala da APC a jihar Kebbi karkashin Gwamna Atiku Bagudu, a yau ba a yin komai tare da shi idan bancin wulakanci".

A Kebbi ta tsakiya kuwa, mun sami bayani yadda wata guguwar kiyayya ta yi gangami kuma ta hade, amma fa bata fara yayyafi ba yanzu, domin dai magoya bayan Alhaji Salisu Jarman Koko sun sha alwashin sai sun rama wa kura da aniyarta, gwargwadon yadda suka ce an tozarta maigidansu da gangan a yanayi da Alhaji Sani Koko ya ce " cin amana da rainin hankali saboda sun san mu masu biyayya ne da son zaman lafiya. Idan ba haka ba babu yadda za'a yi a yi mana irin wannan cin amana  haka kawai domin son rai da ki gaskiya. Allah ya kai mu 2019, Ai dole kowa ya san inda dare ya ayi masa a jam'iayyar APC".

A Masarautar Zuru, jama'a na cike da bakin cikin yadda Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi Samaila Yombe Dabai ya kasa tabuka wani abu domin ganin Gwamanatin Atiku Bagudu ta wadatar da garin Zuru da wutan lantarki, ga kuma rashin kyaun hanyoyin cikin garin Zuru,misali daga randabawal na gidan Yarin Zuru zuwa unguwar GRA, hakazalika rashin kyaun hanyoyin unguwannin  Tudun wada, Zango,Jar kasa, Rikoto, Unguwar Zuru da unguwar Tagwaye wadanda ke cikin yanayi na ban tausayi.

Hakazalika yawancin jama'ar kasar Zuru sun hake Yombe da Gwamna Bagudu domin su saka masu da aniyarsu ta kasa samar da gidan Rediyo balle Talabijin a kasar Zuru, balle ruwan sha wanda bai wadata ba musamman a garin Zuru. Baya ga wadannan zarge zarge, shi kanshi Mataimakin Gwamna na fuskantar nashi kalubale sakamakon yadda wasu matsa ke ganin cewa bai tabuka komi ba a tsawon Mulkinsa tare da Gwamna Bagudu.

Matashin mai suna Isah Wada, yace " abin da nake son ka gane shi ne Yombe ba dan siyasa bane, mutum  ne mai saurin fushi kuma yana  da yawan alfahari da baya da tasiri mu a garemu mutanen Zuru musamman matasa. Zan tabbata maka cewa ba wani abu daya da Yombe  ya yi a cikin Masarautar Zuru domin ci gaban al'umma. An kawo Yombe aka dora mana shi a 2015. Wallahi ni ban ma sanshi ba saidai kawai da na ji cewa Yombe Dabai ne mataimakin Gwamnan jihar Kebbi.Amma ko kai ka gan abu daya da ya yi mana a garin Zuru da kewaye?.. Makarantu, fanfon burtsatse, tallafa wa matasa ko miye Yombe ya taba yi mana a shekararsa kusan hudu a matsayin Mataimakin Gwamna ?".

Bayanai da muka tabbatar da su, sun nuna cewa ba mamaki yawancin jama'a a kasar Zuru sun dawo daga rakiyar jam'iyyar APC  a bangaren zaben Gwamnan jihar Kebbi, musamman idan har Gwamna Bagudu zai sake tsayawa takara da Yombe a zaben 2019, ba mamaki yawancin jama'a za su zabi shugaba  Buhari a mataki na shugaban kasa amma su zabi PDP a matki na Gwamnan jihar Kebbi.

Domin dai har yanzu jama'ar kasar Zuru basu manta da yadda Gwamnatin Atiku Bagudu ta taba su ba, na yadda Gwamnati ta dakatar da wani dan Majalisa Alh Sani Ka'ida mai wakiltar kasar Zuru a majalisar dokoki na jihar Kebbi, wai domin an yi ma tawagar Gwamana Bagudu ihu a cikin garin Zuru a bara. Hakazalika Gwamna Bagudu ya taba Rukayyat Tanko Ayuba, wanda ya kai ga canja mata wurin aiki daga Kwamishinar Ma'aikatar shari'a zuwa Kwamishinar Ma'aikatar cinikayya. Har ila yau, jama'ar kasar Zuru na hake da Bagudu a kan yadda har yanzu  ya ki bin umurnin National Judicial Council NJC da ta amince tare da bayar da umurni Gwamnatin jihar Kebbi ta tabbatar da Asabe Karatu a matsayin babban Jojin jihar Kebbi, amma ya ki.

Wannan lamari ya kara jawo ma Gwamnatin Atiku Bagudu da Mataimakinsa Samaila Yombe mumunar bakin jini a Masarautar Zuru, musamman ga al'ummar Kiristoci da ke da matukar tasiri a siyasar kasar Zuru. Wata Kirista yar asalin garin Zuru da bata son mu ambaci sunanta ta ce " tun farko mumunar kuskure ne kasar Zuru ta yi da ta bari Fadar Sarkin Musulmi ta yaudari mutanenmu a 1976 lokacin da aka kirkiro jihar Sokoto da jihar Niger. Tsohon shugaban kasa na wancan lokaci Janar Murtala Muhammed, ya bukaci Zuru ta zabi jihar da take so a saka ta a ciki, ko jihar Sokoto ko jihar Nigrer ,duba da cewa kasar Zuru ce ta yi iyaka da wadannan jihohi. Sarkin Musulmi na wancan lokaci ya turo tawagarsa da suka lallashi mutanen Zuru domin mu kasance a bangaren jihar Sokoto.

Ba tare da la'akari da banbancin addini da al'adar mutanen Zuru da sauran bangaren Sokoto ba sai shugabannin mu suka biye ma ganin katon rawani, suka bi Sokoto, wannan ne ya kai mu ga halin da muke ciki a yau. Domin da mun bi jihar Niger, wanda muke da al'adu iri daya tsakanin Dakarkari, Gwari, Nupawa da Basawa har da Kambari, da bamu sami kanmu a halin da muke ciki ba a yau a hannun sauran kabilar Hausawa da ke kallon mu kamar sun fi mu wayewa ko bude ido, ba tare da sanin cewa  mun fi su kunya da ragowa ga shugabannin mu bane kawai, amma ba domin kasawa ba. Allah ya kaimu 2019, ai kuri'ar mu 'yancin mu ne ko?".

Wani babban kuskure da Gwamnatin jihar Kebbi tare da jam'iyyar APC ta aikata shi ne yadda har yanzu ta kasa kiran taro domin neman afuwa ga juna. Amma sakamakon wani binciken jin ra'ayin jama'a da muka gudanar, ya nuna cewa abu ne mai matukar wuya jam'iyyar APC tare da Gwamna Bagudu su iya lallashin wadanda suka harzuka sakamakon ababen da suke zargin cewa an yi masu da gangan domin a faranta ma wasu kalilan rai. Gaskiyar lamari shine, jama'a na cike da haushi kuma a shirye suke domin su canja sheka gaba daya domin su rama yadda aka bakanta masu rai.

Wani mai sana'ar Fawa da muka zanta da shi kuma baya son a ambaci sunansa ya, shaida mana cewa " ni dai ba dan siyasa bane kuma bana siyasa, amma gaskiya wannan Gwamnati na jihar Kebbi ita ce Gwamnati da na fi shan wuya a zamaninta, domin na daina ganin kimar Gwamnatin jihar Kebbi saboda yadda take fadin abubuwa kuma bamu gani a kasa. An ce jihar Kebbi ce ta fi noma shinkafa a Najeriya, amma fa ni kam ban gan amfanin haka ba, domin ina sayen kwanon shinkafa da aka noma a nan garin Birnin kebbi a kan Naira 350 sabanin yadda nike sayensa a 2014. Rago da nike saye N30.000 in yanka a kullum yanzu sai na saye shi a Naira 50 ko 60.000. Wallahi ni dai kam gwamma jiya da yau".

Sakamakon binciken mu ya nuna har'ila yau, yadda rudani da guguwar harkokin siyasa musamman a zabukan fitar da gwani na jam'iyyar APC suka rage tagomashi da Gwamna Bagudu yake da shi a idanun jama'a kafin gudanar da wadannan zabuka. Musamman a idanun wasu jama'ar Masarautun Argungu, Gwandu da Zuru. Hakazalikaa, rashin fitowa ta yi ma jama'ar jihar Kebbi bayani karara dangane da matsayin PA Faruku Inabo a cikin gwamnatin jihar Kebbi a yanzu, ya kara haifar da wani katon gibi sakamakon wata jita-jita da ta dade tana zagayawa cewa Gwamna Bagudu ya cire shi daga mukaminsa domin a sami maslaha tsakaninsa da kaninsa Ibrahim bagudu wanda ake zargin cewa yana dan tsami a kan cewa yayanshi Gwamna Bagudu baya kilisar mulki tare da shi kamar yadda tsofaffin Gwamnonin jihar Kebbi suka yi a zamaninsu.

A zamanin Adamu Aliero dai yana kilisar mulki ne tare da kaninsa Abba Aliero, sai kuma Gwamna Sa'idu Dakingari wanda ya sha zakin mulki tare da kaninsa Lawali Dakingari. Amma a zamanin Atiku Bagudu, sai yake shan zakin mulkinsa tare da Faruku Inabo da kuma Zainabu Abu yar lele tare da Uwar gida Aishatu da jama'a ke zargin cewa suna gasar gudanar da tarukka. Domin idan Dr. Zainab ta fito da wani shiri yau, tau masu sa ido suka ce gobe ma sai Hajiya Aisha ta fito da nata, kuma dole ne a yi wadannan ababe cikin darajar gwamnati.

Daga karshe, idan har Gwanatin jihar Kebbi tana son ta mayar da martabarta tare da jam'iyyar APC a idanun wadannan mutane da suka harzuka sakamakon bayani da muka ambato a sama ,

1. Wajibi ne Gwanati ta fito da wani tsari da zai kawo daidaito tare da yafe ma juna, kuma a saka wa wadanda aka yi wa ba daidai ba wani ihsani domin rage radadin haushi da suka tara, musamman a Masarautar Argungu.

2. Shiga tsakanin wadanda suka yi takarar kujerardan majalisa,yin sulhu tsakaninsu tare da ihsani ne kawai zai kawar da yiwuwar aniyar wasu da ke shirin canja sheka su bar jam'iyar APC.

3. Wajibi ne Gwamna Bagudu ya shiga tsakani, domin ya mayar da martabar mataimakinsa da mutuncinsa ke cikin tsaka mai wuya, sakamakon zargin rashin tabuka wani abun a zo a gani kasa a kasar Zuru tun hawansa mulki a 2015. Hakazalika ana zarginsa da kin biyan talakansa kudin aiki da da aka yi masa da gangan, lamari da wasu ke ma kallon zalunci ne da danniya karkashin mulkin APC ta halayen shi mataimakin Gwamna. Misali shi ne yadda ya ki biyan wani Mawallafi hakkinsa na wata hudu da gangan duk kuwa da hujjoji da Mawallafin ya gabatar na tabbacin aikin da aka yi masa.

4. Fayyace wa jama'ar jihar Kebbi gaskiyar matsayin Faruku Inabo, da kuma tabbatar wa jama'ar jihar Kebbi cewa Gwamnati tana yi da shi kuma a bayar da hujjojin cewa Gwamnati tana yi da shi. Ganin cewa ba a ganin Fruku Inabo a yawancin ababen da ke faruwa a gwamnatance a cikin garin Birnin kebbi kamar yadda aka saba ganinshi yana kai koma a can baya. Misali shi ne yadda aka kasa ganinsa a taron bikin zagayowar ranar samun yancin Najeriya, da kuma harkokin fadi-tashi da aka gudanar na zaben fitar da gwani na jam'iyyar APC. Sabanin yadda aka saba ganinsa yana kai komo a can baya. Marmakin haka, Ibrahim Bagudu ne aka lura yana ta kai kawo.

5. Biyan kudaden tsofaffin ma'aikata yan fansho zai yi tasiri kwarai ga nassarar siyasar dan Bagudu a 2019, binciken mu ya nuna rinjayen ma'aikatan gwamnatin jihar Kebbi suna tausaya wa tsofaffin ma'aikatan jihar Kebbi ganin yadda suke ta fadi tashi a kan hakkinsu cikin kuncin rayuwa, sakamakon haka suke fargaba ko za su fada cikin irin wannan damuwa idan su ma sun yi ritaya daga aikin gwamnatin jihae Kebbi.



 Shiga shafinmu na Facebook web.facebook.com/isyakuweb

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0 Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

KANA ZAUNE A BIRNIN KEBBI? WAYAR KA TA LALACE KO KANA BUKATAR FLASHING? 

Garzaya zuwa SENIORA TECH,shago mai lamba 50, hawa na sama gefen hagu,TAUSHI PLAZA , yamma daga gidan marigayi Waziri Umaru,kan Tiltin Ahmadu Bello, Nassarawa, Birnin kebbi. Barka da zuwa gidan sauki wajen gyaran wayar salula a garin Birnin kebbi.

Post a Comment

 
Top