Bayan da Atiku Abubakar ya lashe zaben fidda gwanin dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa, Muhammadu Buhari sun tayashi murna sannan kuma suka ce ba'a taba samun lokacin da gaskiya karara ta bayyana ga 'yan Najeriya akan zaben shugaban kasa ba kamar wannan karin, saboda za'a karane tsakanin mutumin da a gida da waje an san rashawa ta mai katutu da kuma wanda ko kadan ba'a taba samunshi da maganar rashawa ba.
Haka kwamintin ya kara da cewa, Atiku fa kudi ya raba dan sayen kuri'un wakilan PDP wanda ta hakane ya samu nasarar da ya samu dan haka 'yan Najeriya sai su lura idan zasu baiwa irin wannan mutumin dama ya shugabance su da kuma gudanar da dukiyar kasa.
Saidai a martaninshi, Atiku Abubakar ya bayyana cewa, da Buhari na da kwakkwarar shaida akan cewa, Atiku barawone to da tuni ya kamashi, lura da yanda yake cike da son daukar fansa akan mutane.
Yace maganar zabe kuma, ai APC ce ta yi abin kunya, dan kuwa shugaba Buhari ne kadai aka tantance a matsayin wanda yayi takarar zaben fidda gwani duk da cewa akwai 'yan takara biyar dake hamayya dashi, kuma wai akace ya samu kuri'u kusan miliyan 15, ta yaya haka zata kasance in ba da murdiya ba?
Ya kara da cewa, inda zaka san APC akwai matsala, shine yanda matar Buhari, A'isha wadda ta fi kowa saninshi, ta fito ta gayawa Duniya cewa zaben nasu ba adalci.
Yace amma shi kuwa Atiku, zabe aka yi wanda aka nuna kaitsaye a gidan talabijin kuma 'yan takara da dama ne suka yi hamayya dashi wanda aka gudanar da sahihin zabe kuma Atikun ya samu kuri'u 1532.
Yace, rudanin da mutanen Buhari suka shiga da nasarar da Atiku ya samu a zaben fidda gwani ba abin mamaki bane dan kuwa sun san dama haka zata kasance saboda nasarar Atikun na nufin mulkin Buhari ya zo karshe kenan.
Ya kuma kara da cewa, yanzu dai zabi ya rage wa 'yan Najeriya, su zabi dan takara me jini a jika wanda ya samarwa da mutane dubu 50 ayyukan yi a kamfanoninshi masu zaman kansu ko kuma su zabi gawa taki rami(kamar yanda shugaban kasar Amurka ya kirashi) wanda a karkashinshine aka rasa ayyukan yi miliyan 11 sannan kuma Najeriya ta zama hedikwatar talauci ta Duniya.
Post a Comment