Haka kuma Emmanuel, ya ci gaba da cewa, mataiamakin Daraktan kungiyar ‘yan asalin Biafiran (IPOB) Uche Ejiofor ya tabbatar da cewa mutumin da ya gani a faifan bidiyon Kanu ne.
In za a iya tunawa dai tun lokacin da sojoji suka kai farmaki gidansu Kanu ranar 14, ga Satumba, 2017, ba a sake jin duriyarsa ba, tare da iyayensa.
Emmanuel ya ci gaba da cewa, mambobin kungiyar ta IPOB da dukkan mutanen da ke zaune a garin Isiama Afaraukwu sun yi farin ciki da jin wannan labara na cewa, har yanzu Kanu na raye.
Ya ce duk da haka, har yanzu ba za su iya cewa, ga inda iyayen Kanu suke ba.
Ya ce, “Na tabbatar da cewa mutumin da na gani a bidiyon Kanu ne, nag an shi kuma yana addu’a. Saboda haka yau cike muke da farin ciki.”
Post a Comment
Click to see the code!
To insert emoticon you must added at least one space before the code.