*Abubuwa 10 Dake Hana Mata Jin Dadin Jima'i/Gamsuwa ko Sha'awa a Rayuwar Aure*
*Shin kona mamakin mi yasa iyalinka bata da sha'awa? Ko kema kina mamakin mi yasa baki jin dadin jima'i ko baki da sha'awa? Sai ku duba ku gani mai yiwuwa wannan bayanai zasu iya baku haske akan matsalar dake damunku domin neman mafita.
*admin maijidda bello *✍️
hakana faruwa inda zaka sami mace na gudun kwanciyar aure ko bata damu da ayi kwanciyar ba ko kada ayi (duk daya ne a gurinta) saboda koda anyi ma bata jin dadin jima'in sam , ko kuma bata jin dandanonsa irin yanda take tsammani ake ji , kamar yanda sauran mata 'yan uwanta ke jin dadin rayuwar aure da mazajen su.
*admin maijidda bello *✍️
Tana yin kwanciyar aure ne kawai a matsayin wani aiki (duty) na biyan bukatar mijinta ba bukatar taba, kuma ba don tana jin dadi ba ko gamsuwa , saidai kawai don bautar aure ko gudun fushin sabawa al'ada, ko kuma domin kare mijinta daga fadawa tarkon zina.
Hakika akwai mata da yawa da suke cikin wannan yanayin rayuwar aure marar dadi, wanda sun hakura da hakkinsu na jin dadin aure inda wasu matan kuma ke kokarin neman mafita daga wannan matsala ta neman hakkinsu daga mazajensu ko neman magani, koma kokarin fahimtar matsalar dake hana su jin dadin da nufin neman warwarar matsalarsu. Wannan kalubale ne babba.
Anan zamu ari wasu bayanan lafiya domin bada haske ko bayani akan wasu daga cikin dalilan da yasa wasu mata basa da sha'awa, ko basa jin dadin jima'i (salaf suke ji), ko basa jin dadi sosai, ko kuma ma basu taba jin dadin ba a rayuwar aurensu. Wasu dalilai nada alaka da macen, wasu kuma namijin ne.
Sune kamar haka:
1. CIWON SANYIN MARA KO MATSALOLIN MARA DA MAHAIFA:
Kama daga sanyin mara (vaginities/toilet infections, UTI & STDs), yoyon fitsari, 'kululun mahaifa (fibroid), da sauran cututtukan al'aura na daga cikin abubuwan da ka iya hana mace jin dadin jima'i.Misali, sanyin gaba mai zuwa da 'yan 'kananan kuraje cikin farji , na sanya mace taji zafi wajen jima'i yayinda zakari ke kai-kawo cikin farji, wanda sau da yawa masu kurajen basu ma san suna da kurajen ba cikin al'aura, saidai suce suna jin zafi lokacin saduwa. Kurajen suna fashewa saboda da gugar zakari, sai wurin ya zama rauni. Hakan nasa mata tsoron jima'i da ganinsa abin azabtarwa gare su mai maimakon abin jin dadi. Sau tari basu san abinda ya haddasa zafin ba, wanda kuma mai yiwuwa ciwon sanyi.
Ciwon sanyi na iya dakushe sha'awar mace ko namiji. Ciwon sanyi na iya haddasa bushewar gaba (vaginal dryness) wanda alamunsa shine daukewar ni'ima da 'kaikayin gaba. Idan gaba ya bushe zaiyi wahala mace da miji suji dadin jima'i in banda zafi. Haka kuma shima 'kululun mahaifa (fibroid) yakan ci karo da zakari cikin farji sai mace taji wani irin yanayi marar dadi (discomfort) lokacin nishadin aure. Kuma yana danne mahaifa ya hana haifuwa da kuma sanya yawan zubar jini. Don haka neman magani shine Mafita.
2. BUDADDEN GABA:
Rashin tsukakken farji yanda zai damki zakari da kyau domin samar da jin dandanon fata-da -fata a matse. Budadden gaba kalubale ne dake sanya raguwar jindadi tsakanin ma'aurata.
Sau da yawa ma'auratan biyu ba zasu sami gamsuwa ba da kyau, sa'annan macen baza ta iya jin 'kololuwar dadi ba (orgasm). Akwai dabarun kwanciya da magani na zamani da zasu iya magance wannan matsala.
3. KACIYAR MATA (WUCE GONA DA IRI WAJEN YINTA):
kaciyar mata (female circumcision) wacce Wanzan ya yanke beli da yawa fiye da yanda ya dace. Yin hakan na kashe sha'awar mace idan ta girma. Da yawa mata an yanke musu sha'awa a duniya tun lokacinda suna jarirai. Wasu al'adun a duniya suna yanke beli ne kadan, wasu kuma kamar rabi ne ake fillewa, wasu kuma cire shi suke duka, wato yanke shi suke gaba daya. Yanke beli da yawa ko duka matsalace dake hana sha'awa ga mace.
Zamu ci gaba da bayani, ku kasance da shafinmu a koda yaushe ta www.trustposts.com dan jin dadinku..
Post a Comment