An tabbatar da Gwamna mai ci Abdullahi Umar Ganduje a matsayin dan takarar gwamna na jam'iyyar APC a Kano.


Gwamnan da ke neman wa'adin shugabanci na biyu, shi ne dan takara daya tilo a zaben fidda gwanin da aka gudanar ranar Asabar.

Ya lashe zaben ne da yawan kuri'a miliyan 2,740,847 da 'yan jam'iyyarsa ta APC suka kada ta hanyar bin tsarin 'yar tinke.

Wasu dai na ganin tsayawar dan takara daya tilo ya rage wa zaben armashi.

Sai dai kuma mataimakin gwamnan jihar Nasuru Yusuf Gawuna ya ce babu wanda aka hana wa tsaya wa takara domin fafatawa da gwamnan kuma tsarin 'yar tinke da suka gudanar ya nuna sun shirya yin adalci.

Kamar jihohi da dama, a Kano ma an shafe sa'o'i gabanin fara zaben a mafi yawan mazabu, saboda jiran isar kayan aiki, da jami'an zabe da kuma zuwan jami'an gwamnati wuraren zaben.

A bangaren jam'iyyar adawa ta PDP kuma an dage zaben na fitar da gwani ne na kujerar gwamnan jihar Kano, kuma har yanzu uwar jam'iyyar ba ta sanar da tsayar da ranar zaben fitar gwaninta ba wanda zai fafata da gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jam'iyyar APC.
An tabbatar da El Rufa'I a Kaduna.

A jihar Kaduna ma an yi zaben 'yar tinke ne, domin tabbatar da takarar gwamna mai ci Malam Nasiru Ahmed Elrufa'i, kasancewarsa shi ne dan takara daya tilo na kujerar gwamnan a jihar.

A bangaren jam'iyyar adawa ta PDP kuwa, kimanin mutum bakwai ne suka fafata a zaben fidda gwani na takarar gwamnan jihar inda aka yi amfani da tsarin wakilai.
BBChausa.

Post a Comment

 
Top