Daga Haji Shehu

A daren jiya, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana tare da yin liyfar cin abinci da wasu daga cikin Jaruman masana'antar wasa kwaikwayo na Hausa (Kannywood) a fadar mulki ta Aso Rock dake birnin tarayya Abuja.

Kasancewar cewar masana'antar Kannywood tana jihar Kano ne, wasu na ganin cewar gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ne ya kamata ace ya jagorance su zuwa liyafar cin abincin.

Amma abun mamaki sai ga shi gwamnan jihar Kaduna da Filato sune suka jagoranci tawagar zuwa fadar shugaban kasa. Hakan tasa wasu ke danganta lamarin da zargin badakalar Daloli da Jaafar Jaafar ya bankado na gwamna Ganduje.

Yayinda wasu ke cewar kunyar badakalar ce ta sanya gwamna Ganduje tsukewa daga halartar taron, wasu kuma cewa suke gwamna Ganduje na jin kunyar yin Ido hudu da Shugaban kasa Buhari ne tun bayan bayyanar Bidiyon zargin badakalar Daloli.

Post a Comment

 
Top