Daga  DailyNigerian Hausa/ Muhammad Bashir Amin

Yauma kamar wancan Makon tun hantsi ake dakon karasowar daya daga cikin Jagororin Jam’iyyar PDP anan Kano wato Engr. Dr. Rabi’u Musa Kwankwaso wurin taron tattaunawa da samarwa Jam’iyyar PDP Sahihin Dan takarar gwamnan jihar Kano da kowa zai gamsu da hanyar da aka bi wurin samar da shi, sai dai har yanzu Kwankwason bai samu ikon karasowa Ofishin Jam’iyyar PDP ba.

Majiyarmu ta tattauna da wani da ya bukaci a sakaya Sunansa yace; sun sami labarin cewa tuni Kwankwason ya aiko da sakon cewa shi fa ba zai halarci wannan zama ba, kuma ya yi wa Jam’iyyar PDPn barazanar cewa da zarar ya samu labarin an taba masa daya daga cikin mutanan da ya jera don yi masa takara a matakai daban-daban to fa zai yi tsalle ya buga nutso a Jam’iyyar ADC.

Jam’iyyar ta PDP dai ta tsara yau Laraba 10/10/2018 zata zauna a Ofishinta na Legacy House dake Unguwar Maitama Abuja, don samawar Jam’iyyar Dan takarar daya tilo biyo bayan karbar korafi da aka gabatarwa kwamatin amintattun Jam’iyyar Na kasa daga sauran ‘Yan takara masu zawarcin kujerar gwamnan jihar Kano a Jam’iyyar a kakar Zaben shekarar 2019 mai zuwa.

Jam’iyyar ta PDP ta nada Mataimakin Shugaban Jam’iyyar Na Shiyyar Arewa maso yamma, Amasada Ibrahim Kazaure a matsayin wanda zai jagoranci sasanta ‘Yan takarar da suke kalubalantar Zaben fidda gwani Na Jam’iyyar da ya bawa Surukin Kwankwaso Abba Kabir Yusuf Nasara, a matsayin zabe mai cike da rudani da rashin Sahihanci.

Majiyarmu ta rawaito mana cewa akwai Akalla masu jefa kuri’ar raba gardama (Delegates) kimanin mutum hamsin (50) wadanda suka hada da zababbun Shugabannin Jam’iyyar PDP Na Kananan hukumomi talatin da takwas (38) wadanda basu canza sheka ba sun bar Jam’iyyar da Iyayen Jam’iyyar Na jihar Kano wanda ake sa ran yau zasu hallara a Ofishin Jam’iyyar Na Abuja don samar da Sahihin Dan takarar gwamna a kuma maye gurbin Surukin na Kwankwaso da shi da zarar an kammala kada Kuri’ar ta raba gardama, idan kuma Abban ya yi nasarar lashe Kuri’ar raba gardaman zai ci gaba da zama a matsayin Dan takarar gwamna a Jam’iyyar PDP a jihar Kano.

A ranar 2 ga watan Octoba ne dai aka bayyana Surukin na Kwankwaso Abba K. Yusuf a matsayin wanda ya yi nasarar lashe Zaben cikin gida Na Jam’iyyar PDP , an kuma gudanar da zaben a gidan Mahaifin Matarsa wato Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso dake Unguwar Lugard Avenue cikin karamar hukumar Nassarawa dake Kano tare da Dan takarar gwamna daya tilo da ya fito daga wajen Darikar Siyasar Kwankwasiyya.

A wancan lokacin jami’an tsaron ‘Yan sanda sun garkame wurin da aka ayyana don gudanar da zaben wato Sinimar Marhaba, biyo bayan Umarnin da Kotu ta bayar na dakatar da rushe Shugaban Jam’iyyar Na jiha.

Shugaban da ya jagoranci zaben a wancan lokacin, Ezeogu Onouha, ya bayyana cewa an tantance adadin masu kada Kuri’a kimanin mutum dubu hudu da dari daya da talatin 4,130.

Shugaban kwamatin zaben ya dai bayyana Surukin Na Kwankwaso Alh. Abba Kabir Yusuf a matsayin wanda ya yi nasara a zaben da kimanin kuri’u dubu biyu da dari hudu da Ashirin da daya 2,421 inda ya yi nasara akan takwaransa wanda ya zo na biyu, Jafar Sani Bello, wanda ya samu kuri’u 1,258.

Mr Onuoha Ya bayyana Sadiq Wali a matsayin wanda ya zo na Uku da kuri’a 167 inda Salihu Takai ya zo hudu da Kuri’a 95 kamar yadda suka bayyana.

Ibrahim Ali-Amin (Little) ya zo na biyar inda ya samu Kuri’a 51, Akilu Indabawa ya samu Kuri’a 33 inda ya zo na shida.

Post a Comment

 
Top