Uwar jam’iyyar PDP ta yi watsi da dan takararta na mukamin gwamnan jahar Kano, kuma surukin jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, Abba K Yusuf, inda ta tabbatar da Salihu Sagir Takai a matsayin sabon dan takararta a zaben 2019.
Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito uwar jam’iyyar ta dauki wannan mataki ne a ranar Alhamis, 11 ga watan Oktoba biyo bayan nuna rashin amincewa da sauran yan takarar gwamna a jam’iyyar suka nuna game da yadda aka gudanar da zaben fidda gwani a gidan Kwankwaso.
Takai ya samu goyon bayan shuwagabannin jam’iyyar PDP na kananan hukumomin talatin da takwas daga cikin arba’in da hudu da ake dasu a jahar Kano a wani kwarya kwaryan taro da aka yi a Abuja.
Sai dai har zuwa lokacin tattara wannan rahoto, majiyarmu ba ta samu Kaakakin jam’iyyar PDP Kola Ologbondiyan ba, don ta jin ta bakinsa, sakamakon lambobin wayoyinsa duka ba sa shiga.
Sai dai wani dan gani kashenin Kwankwasiyya, kuma aminin tsohon gwamnan jahar Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, Mohammad Digol ya bayyana matakin da PDP ta dauka a matsayin karya doka, inda yace lokacin shirya zaben fidda gwani ya wuce, kuma duk wani taron jam’iyya da aka yi a wajen Kano haramtacce ne.
Idan za’a tuna Yusuf K Abba ya zama dan takarar gwamna a jam’iyyar PDP ne a ranar 2 ga watan Oktoba a wani zaben fidda gwani dake cike da cecekuce daya gudana a gidan surukinsa, Kwankwaso dake Lugar Avenue.
Da fari, jam’iyyar ta yi nufin shirya zaben nata a Marhaba silima, sai dai jami’an Yansandan jahar Kano sun garkame siliman, inda suka ce suna amfani da umarnin Kotu ne da ta hana duk wani tsagin jam’iyyar PDP shirya taro, sakamakon karar da shugaban tsagin PDP, Doguwa ya shigar gabanta.
Naija.ng.
Post a Comment