Wata kotun majistare dake Minna tayi umurnin tsare wani manomi mai shekaru 32, Rilwanu Salisu a gidan yari bayan ya amsa laifin yiwa tsohuwa ýar shekara 78 fyade.

An gurfanar da Salisu ne akan fyade daidai da sashi 282 na kundin doka. A cewar dan sanda mai kara, Mista Daniel Ikwoche, dan tsohuwar, Mukhtar Garba ne ya shigar da karar lamarin ga ofishin yan sandan Nasko a ranar 14 ga watan Satumba.

Ikwoche yace wanda ake zargin mazaunin kauyen Kwada a karamar hukumar Magama, ya shiga dakin tsohuwar, yayinda take bacci sannan ya haike mata inda ya sadu da ita ta karfin tsiya. Sannan kuma cewa ya jiwa tsohuwar rauni sosai inda jini ya balle mata.

Da aka karanto tuhumar da ake masa, ya amsa laifinsa inda ya roki kotu da tayi masa afuwa. Sai dai babban alkalin kotun, Nasiru Muazu ya dakatar da rokon mai laifin saboda kotunsa bata da sauraron haka. Muazu ya umurci yan sanda da su gabatar da kwafin takardar shariar zuwa daraktan doka na jihar don jin shawararsa.

Sannan yayi umurnin ci gaba da tsare mai laifin zuwa lokacin da za’a ji sakamokon shawarar nasa, sannan y adage zaman zuwa ranar 25 ga watan Oktoba. 

Shafin mu na Facebook  http://web.facebook.com/isyakuweb 

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0 Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

KANA ZAUNE A BIRNIN KEBBI? WAYAR KA TA LALACE KO KANA BUKATAR FLASHING? 

Garzaya zuwa SENIORA TECH,shago mai lamba 50, hawa na sama gefen hagu,TAUSHI PLAZA , yamma daga gidan marigayi Waziri Umaru,kan Tiltin Ahmadu Bello, Nassarawa, Birnin kebbi. Barka da zuwa gidan sauki wajen gyaran wayar salula a garin Birnin kebbi.

Hausa.naija.ng
Photo: Dailypost

Post a Comment

 
Top