Tsara Labari: Nasir S. Gwangwazo
Kamfani: Halifa Inbestment
Shiryawa: Nazir Dan Hajiya da Halifa Abubakar Kofar Wambai
Umarni: Ali Gumzak
Jarumai: Ali Nuhu, Hafsat Idris, Rabi’u Rikadawa, Baballe Hayatu, Hadiza Muhammad, Bilkisu Abdullahi, Sani Garba S.K, Bashir Na Yaya, Ladi Muhammad. Da sauran su.
Sharhi: Hamza Gambo Umar.
A farkon fim din an nuna Joda (Hafsa Idris) tare da dan uwan ta (Saifullahi S. Fulani) suna kiwon shanu a cikin wata gona, kwatsam sai daya daga cikin dangin manoma (Baballe Hayatu) yaga shanun su Joda suna ci musu amfanin gona, hakan yasa ya garzaya yaje ya sanar da sauran ‘yan uwan sa, cikin dan lokaci kadan dangin manoma suka yo taron dangi suka shigo rugar fulani suka far musu da sara, hakan yasa fulani ma suka yi cincirindo suka biyewa manoma aka fara dauki ba dadi, ana cikin haka ne mahaifin Joda (Sani Garba S.K) wanda ya labe a jikin wata bishiya yana kallon ruguntsumin da ake tsakanin ‘yan uwan sa fulani da kuma manoma, bai yi aune ba yaji an soka masa takobi a bayan sa, take a wajen ya fadi kasa cikin jini, ganin haka ne yasa mutumin da ya kashe sa din wanda ya kasance kanin sa Imamu (Rabi’u Rikadawa) ya saka hannu ya fizge gurun da ke daure a dantsen (Sani Garba) bayan ya cire gurun ne ya soma matsawa da nufin ya bace amma bisa mamaki sai bai bace ba, ganin haka ne yasa yayi tafiyar sa, bayan ya tafi da dan lokaci kadan sai iyalan (Sani Garba) wato Joda (Hafsa Idris) da kuma mahaifiyar ta (Hadiza Muhammad) suka iso wajen da yake a kwance cikin jini, ganin su ne yasa ya dauki wata layar zana hannun sa na rawa ya mikawa ‘yar sa Joda, bakin sa ya soma rawa yana magana wadda ba’a ji har ya mutu a wajen. Ganin mutuwar sa ne yasa iyalan sa suka rude, take a wajen Innar Joda ta fadi kasa ta suma. Su kuwa bangaren manoma sai babban cikin su ya hada taron gaggawa ya nuna musu rashin jin dadin sa bisa abinda ya faru na kashe-kashen rayuka da akayi bisa dalilin shanun fulanin da suka ci musu amfanin gona. Ya nuna wa jama’ar sa rashin jin goyon bayan sa gami da tabbatar musu da babu makawa yasan fulanin nan ba zasu hakura ba sai sun bibiyi bayan lamarin don daukar fansa. Bayan manoma sun gama taron sai daya daga cikin su (Baballe Hayatu) wanda yazo da labarin cewar shanun manoma sun ci musu amfanin gona sai yake danasanin sanar da ‘yan uwan sa gami da rashin sanar da mai gari run farko, domin bai so rigimar tayi nisa haka ba, yayin da daya daga cikin su (Bashir Na Yaya) shima yake nuna takaicin sa akan kashe masa dan uwa da aka yi. A can bangaren fulani kuwa tun bayan rasuwar (Sani Garba) sai matar sa (Hadiza Muhammad) ta kasance cikin damuwa wanda har rashin lafiya me tsanani ta kwantar da ita, hakan kuma sai ya damu ‘yar ta Joda wadda ke kula da ita, ganin halin da mahaifiyar ta ke ciki ne yasa taje ta sanar da kawun ta (Rabi’u Rikadawa) amma sai ya nuna rashin damuwar sa ta hanyar nuna cewa ya kamata su saba da ciwon Innar Joda wanda ya riga ya zame mata jiki, amma ganin Joda ta damu sai ya tura ta wajen iyalin sa da nufin ta karbo maganin da zata jikawa mahaifiyar ta ta. A wannan lokacin ne Kawou Imamu (Rabi’u Rikadawa) ya hada gangamin jama’ar dake rugar su ya sanar dasu dole su bar garin don su gujewa sharrin manoma, jama’ar cikin wata ruga duk suka amince da shawarar da yazo da ita kuma aka soma shirin tashi daga wannan rugar don komawa wata rugar daban inda zasu sake kafa sabon sansani. Jin cewar za’a tashi daga wannan rugar ne sai Innar Joda (Hadiza Muhammad) ta nuna cewar jikin ta yayi rauni da yawa ba zata iya tafiya ba, wanda dalilin yadda take ji ne yasa ta kira kishiyar ta Haderu (Bilkisu Abdullahi) ta damka mata amanar ‘yar ta Joda. Lokacin da Joda ta fahimci mahaifiyar ta ba zata iya tafiya ba sai ta sanar da Kawun su Imamu, jin hakan kuma ya sanya shi yi wa mahaifiyar Joda bayanin lallai sai ta shirya an tafi da ita, amma sai ta nuna ko a cikin shanun tsohon mijinta ne a dauki wadda zata dauke ta tayi tafiyar a kanta, jin hakan yasa Kawu ya nuna bai san wannan zancen ba, haka dai Innar Joda ta shirya kuma ta taka da kafarta suka bar rugar sukayi hijira.
Bayan sun koma wata rugar ne sai Kawu Imamu ya nuna yana son ya auri Haderu (Bilkisu Abdullahi) ba don komai ba sai don kada iyalan dan uwan sa su wulakanta, kuma yayi haka ne don kada ya raba dukiyar da dan uwansa ya bari ga iyalin sa, hakan yasa ya nuna Innar Joda zata cigaba da zama a gidan sa tana kula da ‘yar ta Joda, shi kuma zai cigaba da kula da dukiyoyin su wanda suka gada daga wajen yayan sa da ya rasu. Ana tsaka da haka ne sai Magaji (Ali Nuhu) yazo garin a matsayin me yiwa kasa gidima (N.Y.S.C) wata rana suna magana da Kawu akan shanun da Magaji din zai rubutawa magani sai yaga Joda, ganin ta ne yasa ya kamu da kaunar ta ya soma bibiyar ta a gona wajen kiwo ko kuma wajen da take tallan fura da nono yana fada mata cewar yana son ta, amma sam ita Joda ba ta sauraron sa saboda Kawu Imamu ya lura da soyayyar dake kokarin kulluwa a tsakanin su hakan yasa ya sanar da Innar Joda kada ta bar Joda ta dinga kula wanda yazo daga birni, bayan Innar Joda ta gargadeta akan ta daina kula shi kuwa sai Joda ta daina shiga sabgar Magaji, shi kuma ganin haka bai sa ya rabu da ita ba har zuwa lokacin da rashin lafiyar mahaifiyar ta ya tsananta, ganin ba su kai ta asibiti bane ya tambayi dalili, amma da suka fada masa rashin kudi ne ya hana a kai ta asibiti sai ya amince da shi zai dau nauyin komai a asibiti, haka aka dauki Innar Joda aka kai ta asibiti aka yi mata aiki gami da bata magani har ta warke, tun daga sannan su Joda basu sake ganin Magaji ba, duk da Joda tana son ganin sa don yi masa godiya, Joda ta soma neman sa har a wajen aikin sa amma bata gan shi ba har sai da ta fidda rai da ganin nasa, sai gashi ya dawo gami da sanar mata da cewar yaje Ziyara can garin su ne. A wannan lokacin ne Joda ta karbi soyayyar Magaji har magana taje wajen Kawun ta Imamu, amma ko da Kawu Imamu ya zurfafa bincike ya gano cewa Magaji yanada nasaba da ainahin manoman da suka kashe musu jama’a, sai ya nuna bazasu bashi auren Joda ba, har ma ya soma kokarin yi masa sharri akan cewar shi ya kashe Mahaifin Joda a rigimar su da Manoma, amma sai Magaji yayi musu akan haka kuma ya nuna sam bai san maganar ba, haka su Kawu Imamu suka kore shi, Magaji bayan ya sake komawa garin su wajen iyayen sa sai yaje musu sa maganar wacce yake so ya aura, amma da sukaji cewar ‘yar asalin fulanin da suka kashe musu dangi ce sai mahaifin sa (Bashir Na Yaya) ya nuna sam bai yarda Magaji ya aura ta ba, amma sai mahaifiyar Magaji (Ladi Muhammad Mutu Ka Rana) ta goyi bayan Magaji gami da kawo dalilin cewar ai suna fulanin an Kashe mahaifin yarinyar da zai aura. A bangaren Joda ma da farko taki bawa Magaji goyon baya saboda jin yana daga cikin wadanda suka kashe mata iyaye, amma sai Magaji ya fahimtar da ita illar gabar dake tsakanin iyayen nasu. Wata rana kwatsam Innar Joda ta shiga dakin Kawu Imamu da nufin jiran shigowar sa don tattauna magana akan auren Joda da Magaji, sai taci karo da gurun tsohon mijin ta wanda mijin nata yabar sallahun cewar duk wanda ya saci gurun shine ya kashe shi, hakan ne yasa ta dauki gurun kuma ta nunawa Joda sannan suka ci alwashin sanar da Magaji don ya taimaka musu akan wannan lamarin.
Abubuwan Birgewa:
1- Labarin ya fadakar, kuma ya tafi kai tsaye zuwa ga sakon da ake son isar wa, sannan kuma ya taba zuciya gami da rike me kallo ta yaddo zai so ganin abinda zai faru a gaba.
2- Sunan fim din ya dace sosai da labarin. (Wata Ruga)
3- An samar da wuraren da suka yi matukar dacewa da labarin, wato (locations) haka kuma an samar da sutturu gami da sauran abubuwan da me kallo zai ga kamar a gaske abin ke faruwa.
4- Daraktan fim din yayi kokari wajen tafiyar da labarin ba tare da ya karye ba, haka kuma yayi kokari wajen dora jaruman a kan turbar da ta dace, domin jaruman sun yi kokari sosai wajen taka rawar gani.
5- An samar da hoto me kyau, haka shima me daukar hoton yayi bajinta wajen nuna kwarewa a aikin sa. Sauti ma ya fita radau ba laifi.
Kurakurai:
1- Lokacin da aka kashe mahaifin Joda wato Ardo Salihi (Sani Garba) me kallo yaga lokacin da ya bawa ‘yar sa Joda wata laya, bakin sa kuma yana motsi ba tare da ya samu damar yin magana ba har ya mutu, amma daga baya sai aka ji Joda tana fadawa mahaifiyar ta cewar kafin rasuwar mahaifin ta yace wanda ya cire gurun sa shine ya kashe shi. Shin a yaushe ya fada mata wannan wasiyyar? Ya dace a nunawa me kallo sanda mahaifin ta ya fadi wannan wasiyyar domin tun daga sanda aka caka masa wuka har ya mutu ba’a ji mahaifin nata yayi magana ba.
2- “Reflector” tayi rawa wanda hakan yasa haske yake daduwa yana raguwa a fuskar (Bashir Na Yaya) a lokacin da Bala (Baballe Hayatu) suke hira yake nuna cewar da yasan labarin da ya kawo cewar ga shanun makiyaya can suna ci musu amfanin gona da ya san hakan zai jawo ayi asarar rayuka da bai fadawa jama’a ba gara ya sanar da me gari. A wannan hirar ne haske yake daduwa yana raguwa a fuskar (Bashir Na Yaya)
3- Bai kamata a nuna Joda (Hafsa Idris) a matsayin budurwa a cikin rugar fulanin kauye ba, saboda idan an yi duba da yadda mutanen kauye suke saurin yiwa ‘ya’yan su aure, Joda ta wuce munzalin da za’a kira ta da budurwa a cikin rugar fulani. Idan kuma lallai ana son nuna ta a matsayin budurwa, to ya dace a nuna cewar miji ne bata samu da wuri ba.
4- Lokacin da Magaji (Ali Nuhu) ya dauki Innar Joda(Hadiza Muhammad) ya kai ta asibiti don a yi mata maganin larurar da ke damun ta, me kallo yaji lokacin da likitan yace tana fama da wata matsala ne a cikin zuciyar ta wadda idan ba’a dau mataki ba komai zai iya faruwa, sannan likitan ya sake cewa za’a yi mata aiki sannan a bata magunguna. Shin wace matsala ce wadda mahaifiyar Joda take fama da ita a cikin zuciyar ta? Matsayin Magaji na dan birni me ilimi ya dace likitan ya sanar da shi irin ciwon dake damun zuciyar mahaifiyar Joda wanda har ta kai ga sai an yi mata aiki, domin haka kawai ba za’a ce mutum na fama da matsala a zuciya wadda za’a masa aiki ba tare da an sanar da irin cutar ba.
5- Lokacin da Innar Joda ta shiga dakin Kawu Mamu ta ci karo da gurun mijin ta a rataye a sama, yanayin yadda ta juya ta kalli wajen har ta dauki gurun yafi kama da cewar ta san da zaman gurun a wajen, bai dace salon juyawar ta ta ya zamo kamar na wadda taji karar waya ko motsin wani abin ba, ya dace ta fara kai hannu wajen da nufin dafa itacen har zuwa sanda hannun ta zai taba gurun sannan ta juyo don ganin abinda hannun ta ya tabo.
6- Me kallo yaga lokacin da ‘yan siyasa su (Isah A. Isah) suka shigo cikin rugar fulani har sai biyu don cimma wata manufa ta su, a farkon zuwan su sun gabatar da kan su, shin me ake son nuna wa a lokacin da aka sake nuno su a karo na biyu bayan sun sake zuwa kauyen? Me kallo yaji lokacin da ‘yan siyasar suke fadawa Kawu Manu cewar yayi shiru da bakin sa zai ji dadin da bai taba ji ba, sai dai kuma har fim din ya kare ba’a nuna dalilin samuwar ‘yan siyasar a cikin labarin fim din ba.
Karkarewa:
Labarin ya fadakar kuma an tabo wasu daga cikin irin matsalolin da suke faruwa a wannan lokacin na rigima a tsakanin Manoma da Makiyaya, sannan kuma an bayyana wata hanya ta auratayya wadda hakan yakan iya sa wa ayi sulhu a tsakani. Sai dai kuma labarin bai dire har karshe ba, duk da kasan cewar za’a yi cigaban sa to ya dace a karshen fim din a rubutawa me kallo cewa akwai cigaban labarin me suna: “Karshen Wata Ruga” yin hakan zai sa me kallo ya soma tunanin cewa zai ga karashen wasu abubuwan wanda ba a karkare su a wannan ba. Wallahu a’alamu!
Post a Comment