Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto ya gargadi tsohon gwamna jihar Aliyu Magatakarda Wamakko
- Tambuwal ya ce idan aka cigaba da matsa masa lamba zai yiwa Wamakko fallasar da sai EFCC tayi mamaki
- Tambuwal ya yi ikirarin cewar akwai abubuwa da dama da ya sani game da gwamnatin Wamakko amma aka roke shi ya rufa masa asiri Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto ya yi barazanar cewar zai yiwa tsohon gwamnan jihar, Aliyu Magatakarda Wamakko tonon silili idan aka kure shi.
A yayin da ya ke yiwa magaya bayansa jawabi yayin da suka zo tarbansa baya dawowarsa daga taron PDP na kasa da aka yi Fatakwal, Tambuwal ya ce akwai wasu abubuwan da Wamakko ya aikata kuma mudin aka kure shi zai fallasa. Tambuwal ya yi barazanar kwancewa mai gidansa Wamako zani a kasuwa
"Lokacin da na zama gwamna, wasu dattawa a jihar sun shawarci ne in rufa masa asiri kuma na amince. Sun san abinda suka aikata kuma muddin nayi fasa kwai, gaba ba za tayi musu kyau ba.
"Amma muddin aka matsa min, zanyi fallasa kuma wasu daga cikinsu ko EFCC za tayi mamakin abinda suka aikata. A bar kaza cikin gashinta," inji Tambuwal.
Gwamnan kuma ya gargadi jam'iyyun siyasa da su dena tayar da fitina a jihar. A cewarsa, Sokoto jiha ce wadda aka san ta da zaman lafiya kuma haka za ta cigaba da kasancewa. Ya shawarci al'ummar jihar su zabi dan takarar da zai biya musu bukatunsu da kawo cigaba jihar idan zabe ya zo.
Sources:naija.com
Post a Comment