Wani labari da ya riske mu ba da dadewa ba na nuni ne da cewa gwamnan
jihar Zamfara dake a shiyyar Arewa maso yammacin kasar nan, Abdulaziz
Yari ya kira wani taron gaggawa na masu ruwa da tsaki a jihar inda
suke tattauna makomar su a siyasance a jihar. Gwamnan na jihar Zamfara
da kuma ke zaman shugaban kungiyar gwamnoni ta Najeriya ya kira taron
ne na masu rike da mukaman siyasa a jihar da ke goyon bayan sa kuma
kamar yadda muka samu hakan bai rasa nasaba da tirka-tirkar da siyasar
jihar ke yi. NAIJ.com ta samu daga majiya mai tushe cewa taron da aka
gudanar ba'a bari kowa ya shiga da wayar hannun sa ba domin gudun kada
abun da suka tattauna ya bulla a waje. Jam'iyyar APC a jihar ta
Zamfara dai na cikin wata cakwakiya biyo bayan rikice-rikicen da ke
faruwa dangane da zabukan fitar da gwani na gwamnan jihar. A wani
labarin kuma, Labarin da ke zuwa mana yanzu ba da dadewa ba na nuni ne
da cewa tuni masu ruwa da tsaki da ma jiga-jigan jam'iyyar PDP a
mataki na kasa suka kammala kulle-kullen baiwa gwamnan jihar Sokoto,
Aminu Waziri Tambuwal tikitin takarar shugaban kasar su a yau. Kamar
yadda muka samu dai, gwamnan na Sokoto yanzu haka yana da goyon bayan
gwamnonin jam'iyya da kuma wasu manya masu fada aji a cikin jam'iyyar
ta PDP. Read more:
https://hausa.naija.ng/1196672-da-dumin-sa-wani-gwamna-a-arewa-ya-kira-muhimmin-taro-yana-fice-daga-apc.html#1196672

Post a Comment

 
Top