A yadda ake tafiya yanzu akwai yiwuwar litar man fetur a fara saida ta akan Naira 205 duba da yadda farashin gangar danyen man ta tashi a kasuwannin duniya a 'yan kwanakin nan idan dai har gwamnatin tarayyar Najeriya ta yanke shawarar dena biyan kudin tallafin man fetur din.
Yanzu dai kamar yadda majiyar mu ta Punch ta ruwaito mana, kowace litar man da ake shigowa da shi daga kasashen waje zuwa Najeriya ta kai Naira 205 wanda kuma hakan ya jaza matsin lamba sosai a bangaren hukumar dake kula da albarkatun man fetur din ta kasa watau NNPC.
Tuni dai dama yan kasuwa a Najeriya suka dena shigo da tataccen man fetur din saboda rashin ribar da ke a cikin harkar yanzu tun bayan da gwamnatin tarayya ta ce ta cire tallafin akan man fetur din a shekarar 2016.
Masana dai na ganin cewa tuni man ya wuce wannan farashin na Naira 145 da gwamnatin ta kayyade amma suka cigaba da biyan kudaden tallafin a asirce, lamarin da ya haifar da cece-kuce a lokutan baya.
Post a Comment