An gargadi 'yan mata a Najeriya su guji tura hotunansu da suka dauka zindir domin aikawa ga masoyansu a kowane irin hali suka sami kansu cikin soyayya. Wata kungiya mai suna  The Due Process Advocates ta gano wasukungiyoyi hudu na masu cin amanar 'yan mata ta hanyar watsa hotunansu da suka aika masu yayin da suke tsirara saboda nuna kauna da biyayya irin na soyayya bisa amana.

The Due Process Advocates ta dauki tsawon lokaci tana bibiyan ayyukan wasu kungiyoyin mutane masu mugun nufi guda hudu a yanar gizo, musamman a shafukan sada zumunta wadanda suka shahara wajen gwanewa kan yin zancen soyayya da 'yan mata a shafukan sada zumunta..

Kungiyar ta ce lamarin yakan fara ne ta hanyar neman 'yan mata kyawawa a yanar gizo, musamman kyawawan mata masana, shahararru ko gwanaye da suka yi fice a kan abin da suke yi ko sana'ar da suke yi. Daga nan sai a wakilta mata wani kyakkyawan matashi ko saurayi da za su fara zance da shi, shi wannana matashi suna kiransa OPERATOR.

OPERATOR zai yi wa yarinyar ko mace kyakkyawan zancen soyayya da zai iya kaiwa ga bayar da kyauta ko ta hanayar tura mata kudi ko wani lamari na kayatarwa. Da yake OPERATOR baya bayar da adireshinsa na gaskiya a shafinsa na sada zumunta, kuma ba hakikanin hotonsa na gaskiya ne zai saka a shafinsa ba. Wanda hakan zai sa ya zama da matukar wuya a yi saurin bankado gasjiyar ko shi waye hakikani.

Daga bisani sukan nemi mace ta aiko masu hotunan ta tsirara domin tabbatar da soyayyarta gareshi, matukar mace ta aika da wannan huto ko hotuna, shikenan sun sami abin da suke so. Domin daga bisani za su fara yi mata barazana cewa ta aiko da kudi idan ba haka ba za su fallasa hotuna da ta aika masu.

Sukan bukaci fiye da kashi % 1000 na duk abin da suka taba ba budurwa ko suka aika mata. Daga bisani macen za ta shiga halin damuwa domin neman wadannan kudade, idan kuwa ta kasa sai su wallafa hotunanta a shafukan sada zumunta kamar yadda wadannan hotuna suka bayyana.

Majiyarmu ta ce The Due Process Advocates tana bayar da hadin kai tare da 'yansanda domin bankado ire iren wadannan mutane da kungiyoyinsu.Kungiyar, har ila yau, ta roki jama'a cewa su rada wa 'yansanda duk wanda suka sani yana gudanar da irin wannan harkar Tuni dai wasu 'yan mata guda hudu suka fada tarkon wadannan mugayen mutane kamar yadda kuka gani a hotuna a sama.


Shiga shafin mu na Facebook facebook.com/isyakuweb

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0

Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

KANA ZAUNE A BIRNIN KEBBI? WAYAR KA TA LALACE KO KANA BUKATAR FLASHING? 

Garzaya zuwa SENIORA TECH,shago mai lamba 50, hawa na sama gefen hagu,TAUSHI PLAZA , yamma daga gidan marigayi Waziri Umaru,kan Tiltin Ahmadu Bello, Nassarawa, Birnin kebbi. Barka da zuwa gidan sauki wajen gyaran wayar salula a garin Birnin kebbi.

Post a Comment

 
Top