Daga Ibrahim Baba Suleiman
Wata jami'a mai suna "ISM Adonai University" a birnin Cotonou ta Benin Republic, ta karrama Manyan Malaman IZALA da digirin digirgir.
Cikin wadanda Jami'ar ta karrama daga sassa daban daban a fadin duniya harda shugaban IZALAR Naijeriya Sheikh Abdullahi Bala Lau, da Babban Sakataren IZALA Sheikh Muhammad Kabir Haruna Gombe, da Sarkin Damaturu, da Sarkin Machina.
Jami'ar ta karrama wadannan Malaman ne bisa jajircewa da sukayi wajen Wa'azi a kasashen Afirka da yankin Turai, da kuma aikace aikacen jinkai ga marayu da nakasassu wadanda ake tallafa musu.
A yanzu Duniyar Musulunci tana Amfanuwa da ilimi da basirarsu a wajen Da'awa. Anyi wannan gagarumin Lamari a yau Asabar A reshen jami'ar dake kasar Togo.
Muna Taya Sheikh (Dr.) Abdullahi Bala Lau da Sheikh (Dr.) Muhammad Kabir Haruna Gombe murna, tare da fatan Allah ya bada ikon jajircewa akan gaskiya, da kuma ikhlasi.
Allah ya kara girma da Daukaka.
Congratulations Akaramakumullah.
HOTO: Musa H. Isah
Post a Comment