Tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya ce akwai dalilai da dama da suka sa shi neman shugabancin kasar a babban zaben 2019.
Ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da
Jimeh Saleh bayan wata ziyara da ya kai ofishin BBC da ke Landan a watan Afrilun bana - wato kafin tsayar da shi a matsayin dan takarar shugabancin Najeriya a jam'iyyar PDP a zaben 2019.

A watan Disamabar bara ne Atiku Abubakar ya fice daga jam'iyya mai mulki ta APC, inda daga bisani ya koma jam'iyyar adawa ta PDP.
Fitaccen dan siyasar ya ce yana so ya tsaya takarar shugabancin kasar ne saboda ya gyara abubuwan da bai iya gyarawa ba, a tsawon shekara takwas da ya yi a matsayin mataimakin shugaban kasar.

"Ina neman shugabancin Najeriya saboda abubuwan da ban iya yi ba don ina mataimakin shugaban kasa, zan samu dama na yi su," in ji shi.

Ya ce zai fara ne da gyara tattalin arzikin kasar, idan ya samu nasarar zama shugaban kasar.
Atiku Abubakar ya ce yana da tabbacin 'yan kasar za su yi na'am da shi ta fuskar yaki da cin hanci da rashawa, inda ya ba da misali da yadda gwamnatinsu ta kafa hukumar EFCC.
'Neman mulki ruwa-a-jallo'
Har ila yau ya ce babu wani da bai zai bincika ba idan ya samu nasarar zama shugaban kasa.

Sai dai ya musanta batun da wadansu suke yi cewa idonsa ya rufe wajen neman shugabancin Najeriya.
Hakazalika ya yi karin haske kan batun hana shi izinin shiga kasar Amurka, inda ya ce ya nemi bizar shiga kasar, "amma sun hana ni."
Sai dai da aka tambaye shi dalilin hana shi bizar ta shiga Amurka ya ce shi ma ba a gaya masa dalili ba.

Alhaji Attiku Abubakar ya kuma musanata cewa an yi gwanjon gidansa a Amurka, inda ya ce dama gidan matarsa ne da ya saya mata, kuma "ita ta sayar da kayanta," in ji shi.
Game da kalaman Shugaba Buhari kan matasa na baya-bayan nan, dan siyasar ya ce ra'ayinsa ya sha bamban da na shugaban, "ba na wa matasan kasar kallon cima zaune."
A karshe ya yi kira ga matasan kasar da su shiga harkokin siyasa, inda ya yi alkawarin ba su kaso 40 cikin 100 na ministocinsa idan ya samu nasarar lashe zabe.

Post a Comment

 
Top