Shahararrar ‘yar wasan kwaikwayi na Nollywood, Anita Joseph, ta bayyana cewa ba za ta taba fitowa a fim din batsa va wato BLUE FILM.
A yayin da ta ke hira da jaridar Vanguard, kyakyawar ‘yar wasar ta ce haramun ne ta fito a irin wannan fim din.
“Allah ya wadai,” ta ce a lokacin da aka tambaye ta ko za ta iya fitowa fim din batsa sakamakon yadda ta ke ma’amala da Judith Mazagwu, wacce aka fi sani da suna Afrocandy.
Ana ganin Afrocandya a matsayin shahararar taruwar fim din batsa.
“Anita ba za ta tava fitowa fim din batsa ba. Kun san mai ya sa ba zan taba fitowa shirin fim din batsa ba? Saboda kudin za kare amma fim din ba zai taba tafiya ba,” ta ce.
“Ba abu ba ne da zan so na yi. Kowane dan Adam namiji da mace yana da abunda ya ke so yayi a rayuwarsa, ban damu da abunda mutane ke yi va.
“Wasu mutane sun ce kin kasance abuyar Afrocandy, sai meye?”
‘Yar wasar ta jaddada cewa ‘yan Nijeriya da dama sun cika munafunci idan abu ya shafi jima’i.
“Mafi yawancinsu suna abunda ya fi haka a bayan kofa. Saboda haka kada a sa ma ni ido, na kasance mai yin abunda ni ke so amma ba zan taba fitowa fim din batsa ba.
“Akwai wasu abubuwa da ba zan iya yi ba. Idan na kasance ina yin sana’a da Afrocandy, sana’ar fim ne ba fim din batsa ba.
“Babu wanda ke da damar fada ma ni kada na yi sana’a da ita saboda labarin da mutane ke fadi a kan ta wannan ya zama na su.”
Post a Comment