Lamarin rashin biyan tsofaffin ma'aikatan Gwamnatin jihar Kebbi ya dau wani salo, bayan hakuri na shekaru, da alkawurra da bangaren Gwamnatin jihar Kebbi ta kasa cikawa domin biyan hakkin wadannan bayin Allah da suka bayar da iya rayuwarsu wajen aikin Gwamnatin jihar Kebbi. Daga karshe dai a yau, wasu tsofaffin ma'aikatan sun yi Alwala suka rungumi Alkur'ani suka karanta a babban Masallacin Idi da ke unguwar Gesse, kuma suka yi Allah ya isa ga duk wanda ya rike masu hakkinsu a jihar Kebbi.

Bayanai daga Alh. Babangida Garba Gwandu, Damburam, yace akwai wasu bayin Allah cikin tsofaffin ma'aikatan da suka rasu yayin da suka jiran a biyasu hakkinsu, sakamakon haka ya bukaci a yi masu addu'a. Kafin daga bisani wani Malami ya gabatar da Addu'a bayan an fara taron da karanta Alkur'ani daga tsofaffin ma'aikatan da suka raba wa junansu Izhu da kowane zai karanta.

Kalli bidiyon bayanin Babangida da bangaren addu'a da aka yi:




Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0 Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

Post a Comment

 
Top